Yanzu yanzu: Yadda Sojoji sukayi awon gaba da shugaban kasar Mali da Firam Minista
Sojoji a kasar Mali a yau Talata sun damke shugaban kasa, Ibrahim Boubacar Keita, da firam Ministansa, Boubou Cisse, daya daga cikin shugabannin Sojin ya bayyana.
"Muna masu fada muku cewa shugaban kasa da Firam Minista na hannunmu" Daya daga cikin Sijin ya bayyanawa AFP.
Ya bayyana cewa an damke su biyun nan a gidan shugaban kasan dake birnin kasar, Bamako.
KU KARANTA: Batanci ga Allah a Kano: Kotu ta yankewa yaro dan shekara 13 daurin shekaru 10 a gidan yari
Gabanin damke shugaban kasan a yau Talata, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, wanda shine wakilin ECOWAS da aka tura sulhunta rikicin Mali, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.
Ya bayyanawa Buhari cewa kungiyar adawa a kasar Mali, M5, ta doge kan bakanta cewa sai shugaba Keita ya yi murabus.
Za ku tuna cewa a watan Yuli, shugaba Buhari da wasu shugabannin ECOWAS sun kai ziyara kasar Mali domin sulhunta bangarori biyu amma ganawarsu da shugaban hamayya, Imam Dicko, ya kare a baran-baran.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng