An buƙaci Buhari ya nemi taimako daga wurin mayu don samar da tsaro da kawar da rashawa

An buƙaci Buhari ya nemi taimako daga wurin mayu don samar da tsaro da kawar da rashawa

Wani mai nazarin Kimiyyan Siyasa, Abdul-Rahoof Bello, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaggawar neman taimako daga wurin mayun Afirka don kawo ƙarshen mastalar tsaro da rashawa.

Tsohon malamin Jami'an da ya bayar da wannan shawarar ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, ya ce ƙalluballen da ke addabar ƙasar za su kai ta su baro kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Bello ya ce lokaci ya yi da Buhari zai yi amfani da irin wannan tsarin na gargagiya domin kare Najeriya daga hare-haren ƴan ta'addan Boko Haram, matsafa da rashawa da ya yi wa kasar katutu.

Tsaro: An buƙaci Buhari ya nemi taimakon daga wurin matsafa
Tsaro: An buƙaci Buhari ya nemi taimakon daga wurin matsafa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ya ce ƙasar ta dade tana amfani da dabara iri guda kuma ba a samun sakamako mai kyau duk da irin addu'o'in da mabiya addinan musulunci da Kirista na kasar ke yi.

DUBA WANNAN: Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC

Ya yi tambaya a kan dalilin da yasa Shugaban ƙasar har yanzu bai yi garambawul a bangaren tsaro na ƙasar ba duk da kiraye-kirayen da al'umma ke yi na a aikata hakan.

Ya tunatar da shugaban kasar cewa Allah (SWT) a cikin Al Kur'ani mai girma ya aike da tsuntsaye daga masu tashi dauke da duwatsu daga gidan wuta su magance wadanda za su kai hari dankin Allah a kan giwaye (Q:105:1-5).

Mai nazarin siyasar ya ce amfani da tsuntsaye da Allah (SWT) ya yi domin magance (Ashiaabil feeli) lamari ne da za a iya kwatanta shi da maita na zamani a ra'ayinsa.

Ya koka kan yadda batun rashawa ke ƙara kazanta a kasar kuma ke danƙwafe nasarorin da shugaban kasar ya samu kuma ƴan adawa na iya amfani da wannan wurin yaƙin neman zaɓe.

"Mai ruwa da tsaki a jam'iyyar ta APC ya shawarci shugaban kasar da kada ya karaya ko ya ja da baya wurin dakile muggan da ke kashe-kashe, garkuwa da mutane, rashawa, mastafa da ke barazanar ganin bayan Najeriya," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel