An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara

An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara

Sarkin Gusau a jihar Zamfara, Dakta Ibrahim Bello ya nada babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, Laftanat Janar Yusuf Tukur Buratai sarautar gargajiya ta Ƙauran Gusau.

Sarkin ya ce an naɗa Buratai wannan sarautar ne saboda jajircewarsa wurin kawo karshen hare-haren ƴan bindiga da ma ta'addanci a yankin arewacin Najeriya.

A jawabin da ya yi yayin rufe bukukuwar ranar sojojin Najeriya ta shekarar 2020 da aka fara a ranar 4 ga watan Yulin wannan shekarar, Sarkin na Gasau ya ce jajircewar sojojin ya saka mutane da dama a arewa suna iya barci da idanun su biyu a rufe.

An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara
An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri

A cewarsa, a baya, mutanen yankin su ba su iya barci cikin dare saboda tsoron harin ƴan bindiga da sauran ɓata gari.

"Na gamsu kuma ina murna da farin ciki bisa tanade-tanade da tsarin da na gani a ƙasa a yanzu, " in ji shi.

Sarkin ya tuna cewa akwai lokacin da mutane ba su iya barci kuma manoma ba su zuwa gonakin su amma a halin yanzu suna iya yin hakan saboda sojoji da aka kawo jihar da kuma kafa atisayen Sahel Sanity a yankin Arewa maso Yamma.

"Allah zai tsare kuma ya kare sojojin mu domin su kare al'umma, Allah kadai zai iya basu nasara duba da shiri da kwarewar da suke nuna wa."

Sarkin ya bayyana cewa ya yi imanin sojojin za su yi nasara a kan ƴan bindigan da sauran ɓata gari a yankin sakamakon atisayen da suka ƙaddamar don kawar da laifuka a yankin.

A yayin taron, an bawa mahallarta kyautuka daban-daban ciki har da wadanda suka shirya bikin da masu jami'an wasu hukumomin tattara bayanai na sirri a Najeriya.

A wani labarin daban, kun ji Yan bindiga sun harbe wani Nasiru Aliyu mai shekaru 37 har lahira a garin Gidangizo da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Mazauna garin sun ce ƴ a bindigan sun kuma raunatta mutane hudu kuma suka yi awon gaba da wasu mata biyu ƴaya da ƙanwa; Amina Mudi, 23 da Zainaru, 20.

Rahotonni sun ce ƴan bindigan sun isa garin Gidangizo ne a kan babura misalin ƙarfe 12.30 na dare suka rika bi gida-gida suna neman abinci da kuɗi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel