Kasar Ireland ta amince da dawowa Najeriya kudin badakalar Abacha €5.5m (N2bn)

Kasar Ireland ta amince da dawowa Najeriya kudin badakalar Abacha €5.5m (N2bn)

Gwamnatin kasar Ireland ta rattafa hannu kan takardan yarjejeniya da gwamnatin Najeriya don dawo da wasu makudan kudi d tsohon sshugaban kasan mulkin Soja, marigayi Janar Sani Abacha, ya boye a kasar €5.5m (N2bn)

Ma'aikatar shari'a da daidaito na kasar Ireland ta bayyana hakan ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

Kudin na cikin $5billion da tsohon shugaban kasan ya wawura tsakanin 1993 da 1998 da yayi mulki.

Ministar shari'ar kasar Ireland, Helen McEntee, tace, "Ina matukar farin cikin rattafa hannu kan wannan takardan yarjejeniyar tsakanin Ireland da Najeriya."

"Wannan shine sakamakon binciken da aka kaddamar na lokaci mai tsawo."

"Hukumar dukiyoyin haram ta taka rawar gani a wannan bincike na duniya inda aka samu damar daskarar da kudi $1bn a fadin duniya, kuma €5.5 million ciki na cikin wani asusun banki a Dublin."

"Hukumar dukiyoyin haram ta daskarar da Kudaden da tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, ya wawura ne a wani banki kasar Ireland a Oktoban 2014."

"Bayan gwamnatin kasar Najeriya ta bukaci kudin shekarar da ya gabata, babbar kotu ta bada daman mayar da kudaden Najeriya."

A cewar ministar, mayar da wadannan kudaden shine karo na farko da kasar Ireland zata yi irin wannan kuma hakan na nuna cewa tana hada kai da duniya wajen yaki da rashawa da taimakawa kasashen da rashawa ya nakasa.

Kasar Ireland ta amince da dawowa Najeriya kudin badakalar Abacha €5.5m (N175m)
Kasar Ireland ta amince da dawowa Najeriya kudin badakalar Abacha €5.5m (N175m)
Asali: Depositphotos

A watan Febariru 2020, Gwamnatin Najeriya, gwamnatin kasar Jersey da gwamnatin kasar Amurka sun rattafa hannu kan yarjejeniyar dawo da kudaden da tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha ya jibgesu a kasashen waje.

Punch ta ruwaito ofisoshin jakadancin Najeriya da na Amurka ne suka bayyana haka a ranar Litinin, inda suka ce yarjejeniyar ta amince da dawo ma gwamnatin Najeriya kimanin dala miliyan 308 mallakin Abacha.

KU KARANTA: Matashin da ya tafi Kano daga Katsina a kasa saboda Ganduje ya samu kyakkyawar tarba

An tura wadannan kudade ne ta bankunan kasar Amurka, inda aka jibgesu a asusun bankin kasar Jersey da sunan wani kamfani Doraville Properties Corporation, wanda yaron Abacha ke shugabanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel