Amnesty ta bukaci a yi watsi da hukuncin kisa da aka yanke wa mawaƙin Kano
- Kungiyar Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta soke hukuncin kisar da aka yanke wa mawaƙi Aminu-Sharif
- Kungiyar kare hakkin bil adamar ta ce kotun Shari'ar ba ta yi wa mawaƙin adalci ba saboda haka ya zama dole ayi watsi da hukuncin
- Babban kotun Shari'ar Kano ta yanke wa Aminu-Shariff hukuncin kisar ne sakamakon batanci da aka ce ya yi wa manzon Allah (SAW)
Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da hukuncin kisar da kotun Shari'a ta Kano ta yanke wa mawaƙi, Yahaya Sharif-Aminu saboda batanci ga Manzon Allah (SAW).
Amnesty ta kuma yi kira ga gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta soke hukuncin kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa mai taken, 'Ya zama dole mahukunta su soke hukuncin kisar da aka yanke wa mawaƙin Kano,' mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Isa Sanusi.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Zulum ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadarsa
Wani sashi na saƙon ya ce, "Ya zama dole mahukunta a jihar Kano su yi gaggawar soke hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke wa Yahaya Sharif-Aminu saboda samunsa furta kalaman batanci da babban kotun Shari'a ta Kano ta yi."
Kungiyar ta ce kwatanta hukuncin da rashin yin adalci inda ta kara da cewa ba a yi wa mawaƙin adalci ba yayin shari'ar.
"Bugu da ƙari, yanke hukuncin kisa bayan ba ayi adalci yayin Shari'a ba ya keta hakkin ƴan adam na rayuwa. Ya zama dole a saki Yahaya Sharif-Aminu nan take ba tare da wasu ƙa'idoji ba," inji shugaban Amnesty ta Najeriya, Osai Ojigho.
An kama Sharif Aminu ne tun a watan Maris bayan wasu masu zanga-zanga sun kona gidan iyayensa kuma suka tafi Hedkwatan hukumar Hisbah ta Kano suka nemi a dauki mataki a kansa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng