'Yan sanda sun kama fasto da audugar al'adar mata

'Yan sanda sun kama fasto da audugar al'adar mata

Rundunar 'yan sanda ta jihar Ondo ta damke wani fasto mai suna Festus Adabayo, a kan zarginsa da ake yi da hada kai da wani mutum mai suna Gbemisola Olafusi, a kan amfani da audugar al'ada wurin tsafi.

Olafusi, matashi ne mai shekaru 20 kuma shine saurayin budurwar.

An zargesa da dauko audugar al'adar da tayi amfani da ita inda ya kai wa Adebayo don sihiri a watan Disamban 2019.

Lamarin ya faru ne a gida mai lamba 17, titin Abayomi Upper Ayeyemi, birnin Ondo.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, bayan watanni kadan da suka dauka audugar al'adar, budurwar ta fara ganin wasu irin abubuwa suna fitowa daga gabanta.

Wannan yasa 'yan uwan budurwa suka fara zargin ko an yi amfani da ita wurin tsafi. Bayan zargin, mahaifin yarinyar ya kai kara ofishin 'yan sandan yankin

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tee-Leo Ikoro, wanda ya tabbatar da kamen wadanda ake zargin, ya ce an fara binciken lamarin.

"Mahaifin yarinyar ya kai kara ofishin 'yan sanda cewa wasu maza sun yi tsafi da diyarsa," kakakin yace.

Ya ce ana bincikar lamarin amma an mika shi gaban sashen bincike na musamman na kisan kai.

'Yan sanda sun kama fasto da audugar al'adar mata
'Yan sanda sun kama fasto da audugar al'adar mata. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa

A wani labari na daban, kungiyar 'yan sa kai ta Diobu a ranar Alhamis, ta damke wani matashi mai shekaru 20 mai suna Uche yayin da yake yi wa yarinya mai shekaru 16 fyade a wani kango da ke titin Ekwe, Mile 3 Diobu, Fatakwal, jihar Ribas.

An gano cewa an kama mutumin a yayin da yake kan yarinyar wurin karfe 1 na rana. Mazauna yankin ne suka kama shi tare da abokansa yayin da suka ja matashiyar budurwar cikin ginin.

Kamar yadda yace, shugaban kungiyar 'yan sa kan, Godstime Ihunwo, an kama wanda ake zargi tare da mika shi hannun 'yan sanda.

Ihunwo ya sanar da Punch Metro cewa jami'ansa sun gaggauta zuwa bayan rahoton da suka samu daga mazauna yankin. Ya kara da cewa, yayin da aka mika wanda ake zargin hannun 'yan sanda, abokansa sun tsere.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel