Da duminsa: Sabbin yan Najeriya 373 sun kamu da Coronavirus

Da duminsa: Sabbin yan Najeriya 373 sun kamu da Coronavirus

Hukumar Takaita Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 373 a fadin Najeriya yau Alhamis.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:37 na daren ranar Alhamis 13 ga Agustan shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta a shafinta na Twitter, ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar a jihohin Najeriya kamar haka:

Da duminsa: Sabbin yan Najeriya 373 sun kamu da Coronavirus
Da duminsa: Sabbin yan Najeriya 373 sun kamu da Coronavirus
Asali: Twitter

Lagos-69

Osun-41

Kaduna-40

Oyo-40

FCT-35

Plateau-22

Rivers-19

Kano-17

DUBA WANNAN: Zulum ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Ondo-17

Ogun-15

Abia-14

Gombe-12

Imo-9

Enugu-7

Kwara-6

Delta-5

Niger-2

Borno-1

Bauchi-1

Nasarawa-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Alhamis 13 ga Agustan shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a Najeriya ya kai 48,116.

An sallami mutum 34,309 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta kashe jimillar mutane 966.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel