Obasanjo ya shawarci matasa su karbe mulki daga tsofaffi

Obasanjo ya shawarci matasa su karbe mulki daga tsofaffi

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bukaci matasan Afirka su kawar da tsofaffi daga madafan iko a kasashen su.

Obasanjo ya shawarci matasan sun riƙa shiga siyasa a dama da su da nufin karbe mulki daga mazajen na jiya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin da ya ke gabatar da wata lakca yayin bikin ranar matasa da ya aka yi ta yanar gizo.

Obasanjo ya shawarci matasan Afirka su fatattaki tsofaffin daga mulki
Obasanjo ya shawarci matasan Afirka su fatattaki tsofaffin daga mulki
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zulum ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Cibiyar cigaban matasa, wata bangare na ɗakin karatun shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da ke Oke-Mosan Abeoluta ne ta shirya taron.

Wadanda suka hallarci taron su fito daga ƙasashen Najeriya, Ghana, Amurka, Mali, Kenya da Afirka ta Kudu.

A cewarsa, muddin ba a tilasta wa tsofaffi barin mulki ba, za su cigaba da rike mulkin ne ba tare da taɓuka wa matasa wani abin azo a gani ba.

Obasanjo ya ce, "Idan ba matse su ku kayi suka sauka daga mulki ba, ba za su sauka ba har da wadanda na shekarun su ya dara 80 za su so su cigaba da zama a kan mulki.

"Irin canjin da nake magana a nan da na ke ganin za mu iya yi shine mu saka a kuɗin tsarin mulkin jam'iyyu cewa dole wani kaso na mukamai matasa ne za su riƙe. Misali ana iya cewa kashi 50 na muƙamai a jam'iyyar masu shekaru ƙasa da 40 ne za su riƙe.

"Ana ma iya inganta abin a ce dukkan waɗanda za a tsayar takara a ƙalla kashi 50 cikin ɗari su kasance wadanda shekarunsu bai haura 40 ba. Wannan fifiko ne mai kyau ga matasa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel