'Dukkan Musulman Najeriya sun aikata laifin batanci': Sakon Shekau a kan hukuncin kashe mawaki a Kano

'Dukkan Musulman Najeriya sun aikata laifin batanci': Sakon Shekau a kan hukuncin kashe mawaki a Kano

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, ya zargi dukkan Musulman Najeriya da aikata laifin batanci.

Shekau ya bayyana hakan ne a matsayin martani a kan wasu rahotanni da su ka bayyana cewa ya soki hukuncin kashe matashin mawaki, Yahaya Aminu Sharif, saboda wallafa mai dauke da kalaman batanci a kan annabi Muhammad.

Legit.ng Hausa ta ci karo da kalaman Shekau a shafi tuwita na fitaccen lauyan nan mazaunin Kano, Barista Bulama Bukarti.

A cikin takaitaccen sakon da Bukarti ya wallafa a shafinsa, ya bayyana cewa; "rahoton cewa Shekau ya soki hukuncin kashe mawaki ba gaskiya bane. Sabanin hakan, Shekau ya goyi bayan hukuncin kisan.

"Hasali ma, ya bayar da shawarar a gaggauta kaddamar da hukuncin tare da janye ma sa damar daukaka kara.

"Kazalika, ya zargi dukkan Muslmin Najeriya da aika laifin batanci," kamma yadda Bukarti ya wallafa.

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa Bukarti ya shawarci rundunar tsaro ta farin kaya da rundunar 'yan sandan Najeriya a kan su binciki zargin cewa daya daga cikin gwamnonin arewa ne ke shugabantar kungiyar Boko Haram.

A ranar Litinin ne kafafen yada labarai su ka wallafa labarin cewa tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN), Ubadiah Mailafia, ya yi zargin cewa daya daga cikin gwamnonin arewa ne babban kwamandan kungiyar Boko Haram.

Mailafiya ya bayyana cewa wani tubabben kwamandan kungiyar Boko Haram ne ya sanar da shi hakan.

'Dukkan Musulman Najeriya sun aikata laifin batanci': Sakon Shekau a kan hukuncin kashe mawaki a Kano
Bukarti
Asali: Twitter

Da ya ke tsokaci a kan wannan zargi na Mailafia, Bukarti ya bayyana cewa akwai bukatar a binciki wannan zargi domin bai kamata a dauki maganar da wasa ba.

"Ina ganin ya kamata rundunar 'yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) su yi amfani da wannan bayani wajen tatsar karin bayanai daga wurin Mailafia a kan zargin da ya yi.

DUBA WANNAN: Bidiyo: NAF ta lalata cibiyar sufurin kungiyar Boko Haram, an kashe dumbin mayaka

"Matukar sun tabbatar da gaskiyar zargin da ya yi, ya kamata su tona asirin wannan gwamna, sannan a tsige shi, a gurfanar da shi a gaban kotu.

"Idan kuma Mailafia ya yi zargin ne babu tushe, shi ma ya kamata a hukunta shi. Amma, bai kamata a yi watsi da zargi mai nauyi kamar wannan ba," a cewar Bukarti, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Lauyan ya cigaba da cewa; "matukar Mailafia gaskiya ya fada, bayanansa za su taimaka sosai wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ma su daukan nauyin kungiyar.

"Idan kuma karya ya tsara, kalamansa za su kasance ma su hatsari ga tsaron kasa da zaman lafiya a tsakanin kabilun Najeriya, musamman idan aka yi la'akari da zaman doya da manja da ake yi a tsakanin sassan kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel