Buhari ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban hukumar NBC

Buhari ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban hukumar NBC

Bayan kammala taronsa da shugabannin hukumomin tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata 11 ga watan Agusta ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban Hukumar Kula da Iyakokin Kasa, NBC.

A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya Boss Musatapha, nadin Adaji za ta fara aiki ne daga ranar Juma'a 7 a watan Agustan 2020.

Shugaban sashin watsa labarai na NBC, Ovuakporie ya ce sabon shugaban zai yi waadi ne na shekaru hudu.

Buhari ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban hukumar NBC
Buhari ya nada Adamu Adaji a matsayin shugaban hukumar NBC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci"

Wani sashi na wasikar ta ce: "Ina farin cikin sanar da kai cewa Muhammadu Buhari, Shugaban Tarayyar Najeriya ya amince da nadin ka a matsayin Direkta Janar na Hukumar Kula da Iyakokin Kasa na tsawon shekaru hudu...

"Nadin zai fara aiki ne daga ranar 7 ga watan Agustan 2020, kuma za a fara biyan ka hakokin ka da albashi kamar yadda ya ke a karkashin doka ta albashin maaikatan gwamnati ta shekarar 2008."

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da ke yankin arewa maso gabashin kasar a matsayin mayunwata da ke neman abinci da za su ci.

Da ya ke magana yayin taron da ake gudanar da fadar shugaban kasa a ranar Talata, Buhari ya ce shugabannin hukumomin tsaron sun yi iya kokarinsu amma akwai bukatar su kara kaimi a bangaren tattara bayannan sirri.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugabannin rundunar sojoji, hukumomin tattara bayanan sirri da mambobin kwamitocin tsaro da wakilan kungiyar gwamnonin Najeriya sun hallarci taron.

Shugaban kasar ya bayyana damuwarsa a kan yadda 'yan ta'addan ke samun kananan makamai duk da rufe iyakokin kasa da aka yi.

"Yan taadan suna nan a cikin kasar nan. Ta yaya har yanzu suke samun kananan makamai? kamar yadda kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya jiyo shugaban ta tambayan shugabanin tsaron.

"Ina farin ciki domin akwai hadin kai tsakanin hukumomin tsaro. Na umurci shugabanin tsaron su rika ganawa da juna kafin taron Kwamitin Tsaro ta Kasa.

"Hukumomin tsaron mu suna da kayan aiki; duk da cewa suna bukatar kari amma dai suna iya kokarin su akwai bukatar inganta tattara bayanan sirri da fassara ta.

Da ya ke karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa 'yan taadan sun fi sojoji makamai, an ruwaito shugaban kasar ya ce abinda ya yi saura cikinsu: "mayunwata ne masu farautar abinda za su ci, suna sata a shaguna, kasuwanni suna kashe mutanen yayin hakan."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel