Tubabben ɗan bindiga ya fada mana daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya - Mailafia

Tubabben ɗan bindiga ya fada mana daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya - Mailafia

Tsohon mataimakin gwamnan CBN kuma mai ruwa da tsaki a Kudancin Kaduna, Dr Obadiah Mailafia ya ce shi da wasu masu ruwa da tsaki a yankin sun tattauna da tubabbun yan bindiga kuma sun fada musu daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya.

Mailafia ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Nigeria Info FM a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2O2O.

Tubabbun dan Boko Haram ya fada mana daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya - Mailfia
Dr Obadiah Mailafia
Asali: Twitter

Kalamansa;

"Bari inyi bayyana wasu abubuwa domin wasu daga cikin mu muna binciken sirri mu ma. Mun gana da wasu daga cikin yan bindiga da suka tuba, daya ko biyu daga cikinsu. Mun tattauna ba sau daya ba, ba biyu ba.

"Sun fada mana cewa daya daga cikin gwamnonin jihohin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya.

"Boko Haram da yan bindiga duk daya ne a Najeriya. Suna da tsari mai sarkakiya da wuyan gane wa.

"A lokacin kullen korona, jiragen su na ta zirga zirga suna kai makamakai da kudade zuwa sassa daban daban a kasar kamar babu dokar kulle.

DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

"Sun riga sun isa kudu. Babu inda babu su. Sun ce mana idan sun gama kai hare hare kauyuka, za su shiga mataki na biyu. Mataki na biyu shine za su fara kai hari birane suna zuwa gidan manyan mutane suna kashe su. Ina tabbatar maka, wannan shine tsarin su.

"Zuwa shekarar 2022, suna son su fara yakin basasa a Najeriya. Kada ku dauka abinda na ke fadi wasa ne. Na yi digiri na ta 3 a Jami’ar Oxford. Ni kuma kwararren ma’aikacin banki ne. Ba mu fadin shashanci.

"Kada kayi wasa da abinda na ke fada maka."

Da aka tambaye shi ko gwamnan da ya ambata da farko, tsohon gwamna ne ko mai ci yanzu, Obadiah ya ce.

"Yana kan mulki yanzu. Ya ce daya daga cikin gwamnonin ne kwamandan Boko Haram a Najeriya kuma ba kudi suke nema ba, suna da isassun kudi."

Ga dai bidiyon hirar nan a kasa;

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel