Mun fitittiki yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, jihar Borno kawai suka rage - Buratai

Mun fitittiki yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, jihar Borno kawai suka rage - Buratai

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa jami'ansa sun fitittiki yan ta'addan Boko Haram daga dukkan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya face jihar Borno.

Buratai ya bayyana hakan ne yayinda ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2020, Premium Times ta gani.

Hafsan Sojan, ya kara da cewa yanzu haka jami'ansa na amfani da labaran leken asiri domin kawar da yan ta'addan daga Borno.

"Babu yan Boko Haram a sauran jihohin dake makwabtaka. An fitittikesu, yanzu suna boye a jihar Borno,"

"Muna aiki tare da masu fararen hula da sarakunan gargajiya, abinda muke bukata kawai shine hakuri. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba." ya bayyana a jawabin da kakakin Buhari, Garba Shehu ya fada.

Duk da wannan ikirari da Buratai ke yi, a watan Mayun nan yan ta'addan Boko Haram sun kai hari garin Dapchi, a jihar Yobe. Gabanin nan ma sun kai wani garin Babangida a jihar a watan Febrairu.

Mun fitittiki yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, jihar Borno kawai suka rage - Buratai
Mun fitittiki yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, jihar Borno kawai suka rage - Buratai
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bankin Duniya ya amince da taimakawa Najeriya da kudi $114.28m domin kiyaye, gano da kawar da barazanar cutar Korona musamman a jihohin Najeriya

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya daura laifin rashin samun nasarar yakin yan ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawarsu da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yamma a fadarsa dake Aso Villa.

Ya kara da cewa cutar Korona ce ta kara tsananta lamarin.

Amma ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda matsalar tsaro ke tsananta fiye da yadda ya samu abin lokacin da ya dau ragamar mulki.

"Muna da matsalan rashin kudi da rashin tsaro. Kun san gado mukayi. Amma ya kamata Al'ummar Arewa maso yamma su godewa abinda gwamnatin nan tayi."

"Ina tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta. Rashin kudi ya zame mana kalubale." Buhari yace

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel