Karin 'yan Najeriya 290 sun kamu da korona, jimilla 46,867
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 290 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:27 na daren ranar Litinin 10 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 290 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: Twitter
Lagos-82
Plateau-82
Oyo-19
FCT-18
Edo-16
Kaduna-15
Enugu-9
Ogun-9
Kano-8
DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel
Kwara-8
Cross River-5
Ondo-5
Rivers-5
Ekiti-4
Imo-3
Borno-2
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Litinin 10 ga watan Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 46,867.
An sallami mutum 33,346 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 950.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng