Bankin duniya ya amince da baiwa Najeriya $114.28m don yakar cutar Korona

Bankin duniya ya amince da baiwa Najeriya $114.28m don yakar cutar Korona

Bankin Duniya ya amince da taimakawa Najeriya da kudi $114.28m domin kiyaye, gano da kawar da barazanar cutar Korona musamman a jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya.

Bisa jawabin da bankin ya saki ranar Juma'a, kudin taimakon ya hada da bashin $100 million daga kungiyar cigaban kasashen duniya IDA, sannan tallafin $14.28million daga asusun lamunin annoba na gaggawa.

Jawabin ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafin ga jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya Abuja, ta kwamitin shiryawa da dakile cutar COVID-19 watau CoPREP.

Hakazalika yace shirin zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar Korona cikin unguwanni ta hanyar samar da dabaru na musamman.

"Najeriya ta zange damtse wajen dakile yaduwar cutar COVID-19, amma akwai bukatar sauran aiki a jihohi, wadanda ke gan gaba wajen wannan yaki." Diraktan bankin duniya na Najeriya, Shubham Chaudhuri, yace

"Wannan shiri zai taimakawa jihohi da kayan aiki da taimakon kudi domin karfafasu wajen yaki da cutar." Ya kara

Chaudhuri ya ce shirin zai bada kudi wajen sayan kayayyakin asibiti, magunguna da gwajin cutar domin rabawa jihohi dangane da irin bukatarsu.

Bayan haka, ya ce dukkan jihohin Najeriya 36 na da shiri da hukumar NCDC ta shirya musu kuma tuni an raba kudade wa jihohi 23.

Bankin duniya ya amince da baiwa Najeriya $114.28m don yakar cutar Korona
Bankin duniya ya amince da baiwa Najeriya $114.28m don yakar cutar Korona
Asali: Depositphotos

A watan Yuni, Bankin Duniya ya ce annobar cutar COVID-19 da kuma karyewar farashin mai a kasuwar Duniya ya jawo tattalin arzikin Najeriya zai shiga cikin matsalar da aka dade ba a ga irinta ba.

Nazarin da babban Duniya yayi ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai shiga irin halin da ya samu kansa a tsakiyar shekarun 1980. A wancan lokaci soji ne su ke rike da mulki a kasar.

A wani jawabi da babban bankin ya fitar mai taken: “Najeriya a lokacin annobar COVID-19: Shirya tubulin babbako da tattalin arziki’, an yi hasashen tattalin Najeriya zai tsuke da – 3.2% a 2020.

IMF mai bada lamuni a Duniya ta na ganin tattalin kasar zai motsa ne da maki – 5.4% saboda annobar COVID-19. An yi wannan hasashe na a kan kasar za ta ci karfin COVID-19 a karshen bana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel