Bidiyo da Hotuna: Ƴar Indimi ta auri biloniyan ɗan sarki, Malik Ado-Ibrahim
Adama Indimi, diyar hamshakin attajirin dan kasuwa, Muhammad Indimi na za ta auri biloniyan ɗan sarki, Malik Ado Ibrahim, wanda ya kafa kamfanin Bicernergy.
Malik ne yarima mai jiran gado a masarautar Ohinoyi na yankin Ebira a jihar Kogi ta Najeriya.
An fara bukukuwan daurin aurensu ne a daren ranar Juma'a 7 ga watan Agusta a Maiduguri da saka lalle.
Za a daura auren a yau Asabar 8 ga watan Agustan shekarar 2020 misalin karfe 10 na safe.
Adama da Yarima Malik sun fara soyayya ne kimanin shekara guda da ya gabata kafin suka yanke shawarar za suyi aure.
A baya, Adama ta taba yin soyaya da shahararren mawakin Najeriya, Dbanji kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.
Ga dai kayatattun hotunan yadda aka yi sa lallen a daren ranar Juma'a a Borno.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Matar Ahmed Musa ta haifi ɗa namiji

Asali: Twitter
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng