Karin 'yan Najeriya 443 sun kamu da korona, jimilla 45,687
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 443 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:26 na daren ranar Juma'a 7 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 443 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: Facebook
Plateau-103
Lagos-70
FCT-60
Ondo-35
Edo-27
Rivers-27
Kaduna-20
DUBA WANNAN: Yan sanda sun kama Manjo ɗin Soja na bogi ɗauke da wiwi masu yawa (Hotuna)
Osun-19
Borno-18
Oyo-18
Kwara-11
Adamawa-9
Nasarawa-7
Gombe-6
Bayelsa-4
Imo-4
Bauchi-2
Ogun-2
Kano-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Juma'a 7 ga watan Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 45,687.
An sallami mutum 32,637 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 936.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng