Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai Kudancin Kaduna
Kungiyar gwamnonin Arewa, NGF, a ranar Alhamis ta yi tir da harin da aka kai a Kudancin Kaduna a baya bayan nan inda aka kashe kimanin mutum 22 a daren ranar Laraba.
Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Dr Makut Macham ya fitar ya bayyana harin a matsayin abin bakin ciki.
Ya nuna damuwarsa kan yadda har yanzu ba a riga an kamo yan bindigan da suka kai harin a kauyukan Atyap guda hudu a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Asali: Twitter
Mr Lalong ya nuna damuwarsa kan yadda ake cigaba da kai hare haren duk da irin kokarin da gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro suke yi na kawo karshen lamarin.
DUBA WANNAN: Soja da ta yi ciki bayan ƴan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara kan korarta daga aiki
Ya ce hare haren da aka kai wa kauyukan ya nuna cewa baya ga zaluntar mazauna kauyen da suke yi, bata garin sun dage domin ganin sun dakile kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi don samar da zaman lafiya.
"Muna bakin cikin afkuwar hare haren da zubar da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Muna Allah wadai da hakan.
"A yayin da muke kira ga hukumomin tsaro su kare dage wa don kama bata garin, muna kira ga mazauna yankunan su taimakawa jamian tsaro da bayannan sirri da zai taimaka a kama bata garin," in ji shi.
Ya ce duk wata kungiya da ke ganin an mata ba daidai ba ta shigar da korafin ta ta hanyar da ya dace a maimakon tayar da zaune tsaye da rikici.
Shugaban NGF din ya mika taaziyarsa da wadanda rikicin ya shafa da gwamnatin jihar Kaduna. Ya kuma yi alkawarin taimakawa Gwamna Nasir El Rufai wurin aiki tare da wadanda abin ya shafa don kawo karshen rikicin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng