Karin 'yan Najeriya 354 sun kamu da korona, jimilla 45,244
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 354 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:34 na daren ranar Alhamis 6 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 354 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: Facebook
FCT-78
Lagos-76
Kaduna-23
Ebonyi-19
Oyo-18
Nasarawa-17
DUBA WANNAN: Soja da ta yi ciki bayan ƴan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara kan korarta daga aiki
Rivers-17
Delta-16
Kwara-15
Akwa Ibom-13
Edo-12
Ogun-12
Plateau-11
Kano-9
Bauchi-6
Borno-6
Ekiti-6
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Alhamis 6 ga watan Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 45,244 .
An sallami mutum 32,430 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 930.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng