Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon

Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon

Manyan abubuwan fashewa tamkar bama-bamai biyu sun rikita babbar birnin Lebanon, Beirut ranar Talata, 4 ga Agusta, inda dimbin mutane suka rasa rayukansu kuma da dama sun jikkata.

Wani rahoton BBC ya bayyana cewa shugaban harkokin tsaron cikin gidan kasar ya ce Bama-baman sun tashi ne a unguwar da akayi ajiyar kaya masu iya tashin Bam.

Tuni dai Firam Ministan kasar, Hasan Diab, ya alanta ranar Laraba matsayin ranar makoki.

Ministan lafiyar kasar, Hamad Hassan ya ce kimanin mutane 2,500 sun jikkata.

Ga jerin abubuwa 5 da muka sani kawo yanzu:

1. Akalla asibitoci uku sun kone kurmus

2. Akalla mutane 100 sun mutu kuma akalla 2,500 sun jikkata, cewar ministan lafiya

3. Akwai yan kasar Phillippines biyu da dan kasar Australiya daya cikin mamata

4. Kasashen Iran, Cyprus, da Malaysiya sun bayyana niyyar taimako

5. An gano sinadarin Ammonium nitrate NH4NO3 ne ya sabbaba fashewar

6. An ajiye Ammonium nitrate NH4NO3 a tashar ruwan ne tun shekarar 2013

Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon
Ammonium Nitrate
Asali: Twitter

Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon
Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon
Asali: Getty Images

Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon
Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da annobar da ta aukawa kasar Lebanon
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel