Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a hedkwatar ECOWAS dake Abuja

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a hedkwatar ECOWAS dake Abuja

Wasu ofishohi a hedkwatar al'ummar tattalin arzikin arzikin kasashen Afrika ta yamma watau ECOWAS dake Abuja sun ci bal-bal yayinda gobara ta balle ranar Talata.

Duk da cewa ba'a samu cikakkun bayani game da abinda ya sabbaba gobaran ba kawo yanzu da ake kawo rahoto, majiyan jaridar Thisday ya bayyana cewa an samu nasarar kashe wutar.

Yayinda aka bukaci karin bayani kan abinda ya faru, ya ce bai da izinin manyansa yayi magana kan lamarin.

"Ba ni wani bayani. Ban ma da izinin magana kan lamarin, ba'a amince min inyi tsokaci a kai ba. An yi gobara, na samu labari saboda mutane sun tambaya."

" Na kira wasu masu ruwa da tsaki kuma na samu labarin an kashe wutar," Cewar Majiyar.

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a hedkwatar ECOWAS dake Abuja
Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a hedkwatar ECOWAS dake Abuja
Asali: Facebook

Saurari karin bayani....

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel