Ban damu da tazarce ba, ko wa'adin nan na karasa Alhamdulillah, amma ba zan yi shiru ba - Zulum

Ban damu da tazarce ba, ko wa'adin nan na karasa Alhamdulillah, amma ba zan yi shiru ba - Zulum

- Dalilin da yasa ba zan yi shiru ba, Zulum ya yi bayani ga gwamonin APC

- Ya ce ba laifin Buhari ko Buratai bane

- Gwamnoni APC sun jaddada masa goyon baya

A ranar Lahadi, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyanawa gwamnonin da suka kawo masa ziyara cewa ba zai iya shiru kan kisan al'ummarsa ba, ya ce ya yi alkawari tsakaninsa da Allah ya kare rayukan al'ummar Borno.

Zulum ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagoranicn gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu.

Gwamnonin sun kawo masa ziyarar jaje bisa harin da aka kai masa a garin Baga, karamar hukumar Kukawa, ranar Laraba, 29 ga Yuli, 2020.

Ban damu da tazarce ba, ko wa'adin nan na karasa Alhamdulillah, amma ba zan yi shiru ba - Zulum
Ban damu da tazarce ba, ko wa'adin nan na karasa Alhamdulillah, amma ba zan yi shiru ba - Zulum
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fashewar Bam ya kashe yara shida a Burkina Faso

Gwamna Zulum ya bayyana takaicinsa kan yadda adadin masu zama a sansanin gudun hijra ke tashi, ya ce akwai bukatar mutane su koma gidajensu tun da a samu zaman lafiya.

"Muna da al'umma da yawa da basu iya zuwa gonakinsu, kuma talauci ne babban ummul -haba'isin wannan ta'addancin."

Abinda muke bukata shine inda aka samu dan zaman lafiya mutane su koma gidajensu. Saboda su iya komawa sana'o'insu na rayuwa."

"Wajibi ne Sojoji su tabbatar da hakan kuma ba zan daina magana a kai ba. Ban zan gajiya ba, ba zan yi kasa a gwiwa ba kuma zan jajirce, Allah kadai ke bada mulki. Ni ba tazarce nike so ba, idan Allah ya taimakeni na karasa wa'adin nan Alhamdulillah."

"Amma a matsayina na gwamna in yi shiru yayinda mutane mliyan shida su mutu, ba zan ji dadi ba. Wannan alkawari ne tsakanina da Allah cewa zan yiwa al'umma ta gaskiya." Zulum ya fadi.

A bangare guda, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa akwai masu yiwa yaki da rikicin Boko Haram a Arewa maso gabas zagon kasa kuma ya kamata shugaban kasa ya san gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel