Mutum 15 sun tsira yayin da gini ya ruso a Kano

Mutum 15 sun tsira yayin da gini ya ruso a Kano

Musiba ta auku yayin da gini ya ruso a kan wasu mutane mazauna unguwar Kurnar Asabe da ke karamar hukumar Dala ta jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, an tafka gagarumar sa'a idan aka samu mutum daya ne kacal ya jikkata yayin da mutum akalla 15 suka tsallake rijiya da baya.

Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar Kano, Mista Sa'idu Muhammad, shi ne ya ba da tabbas kan aukuwar wannan mummunan tsautsayi.

Ya ce ibtila'in zubewar ginin ta auku ne da misalin karfe 12.00 na dare a layin Dangawan Jingau da ke unguwar Kurnar Asabe.

Babban jami'in ya shaidawa manema labarai cewa, wani mutum mai suna Abdurrashid Danjuma, mai shekaru 45, ya samu raunuka yayin da ginin ya rufto a kansa.

Muhammadu ya ce a halin yanzu Danjuma yana samun kulawar kwararru na lafiya inda suke bashi magani a gadon wani Asibiti.

Yayin da ake ceto mutanen da gini ya ruso kansu a Kano
Hoto daga jaridar This Day
Yayin da ake ceto mutanen da gini ya ruso kansu a Kano Hoto daga jaridar This Day
Asali: Twitter

Wani karamin jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari ya yayin da ya ke kokarin tashi sama a hanyarsa ta zuwa kasar Australia a ranar Asabar kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Hatsarin jirgin saman ya tona asirin wasu masu safarar miyagun kwayoyi da ke Melbourne kuma an kama mutane biyar da ake zargin suna da alaka da masu safarar kwayoyi a Italiya.

Jirgin kirar Cesna wadda aka cika makil da kilogram 500 na hodar-iblis wato koken ya fado kasa ne yayin da ya ke yunkurin tashi daga wani karamin filin jirgi da ke Papua New Guinea a ranar 26 ga watan Yuli.

'Yan sandan Australia cikin sanarwar da suka fitar sun ce, "Akwai alamun hadama a cikin harkokin kungiyar ta masu safarar miyagun kwayoyin" inda suka ce bisa ga alamu nauyin hodar-iblis din ne ya hana jirgin tashi sama.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kama saurayin da ya yi wa 'yar shekara 2 fyade

Ana tuhumar mutum biyar din da aka kama a Queensland da Victoria da laifin hadin baki don safarar hodar Iblis kilogram 500 da wasu laifan daban masu alaka da safarar kwayoyin.

Za a iya yi wa kowannensu daurin rai da rai idan kotu ta same su da aikata laifin da ake tuhumarsu.

An kama matukin jirgin bayan ya kai kansa wurin yan sanda. Mahukunta sun ce jirgin ya taso ne daga wani karamin gari mai suna Mareeba da ke Papua New Guinea a arewacin Queensland amma ya yi lambo hukuma ba ta gan shi ba.

Daga bisani an gano hodar Iblis din da jirgin ya dako a ranar Juma'a bayan bincike a yankin. An kiyasta kudinsa zai kai Dallar kasar Australia miliyan 80 wanda ya yi daidai da Dallar Amurka miliyan 57.

Mutanen da aka kama masu shekaru 31, 36, 31, 33, da 61 duk ana tuhumarsu da laifuka daban daban.

Mutum na farko ana tuhumarsa da safarar kwayoyi da almundanar kudi fiye da Dallar Australia Miliyan 1. Yan sanda sun kuma kwace wasu kadarorinsa da kudinsu ya kai Dallar Australia Miliyan 3.5.

Wannan kamun da yan sandan suka yi na yana da cikin kamu mafi girma na muggan kwayoyi a tarihin kasar ta Australia.

A shekarar 2016 an taba kama wata hodar-iblis din mai nauyin kilogram 500 a New South Wales.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: