Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta yi tsokacinta na farko kan jawabin Mamman Daura

Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta yi tsokacinta na farko kan jawabin Mamman Daura

Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan kan kiran da aminin shugaba Muhammadu Buhari, Mamman Daura, yayi cewa a daina amfani tsarin zagaye a kujeran shugaban kasa.

Mamman Daura ya ce kawai a bi cancanta.

Daura ya bayyana hakan ne a hirar da yayi ga BBC Hausa a makon da ya gabata inda kungiyoyi daban-daban sukayi masa martani.

Shekaru 20 yanzu kenan ana amfani da tsarin zagaye a kujeran shugaban kasa tsakanin kudu da Arewa.

A tsokacin farko, fadar shugaban kasa a ranar Laraba ta ce jawabin Malam Mamman Daura ra'ayinsa ne kawai ba na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na sada zumunta inda yace: "Yana da muhimmanci mun bayyana kamar yadda wanda akayi hira da shi ya ambata inda yace maganganun da yayi ra'ayiyinsa ne, amma, ba na shugaban kasa ko gwamnatinsa."

Garba Shehu ya ce mutane sun yiwa jawabin mumunan fassara.

KU KARANTA: Kowani mutum 1 cikin mutane 10 a jihar Kaduna na shan kwaya

Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta yi tsokacinta na farko kan jawabin Mamman Daura
Da duminsa: Fadar shugaban kasa ta yi tsokacinta na farko kan jawabin Mamman Daura
Asali: UGC

Wannan ya biyo bayan tsokacin kungiyoyi irinsu Middle Belt Forum, Ohanaeze Ndigbo, Afenifere da South-South Elders’ Forum ta mutanen Arewa, Ibo, Yarbawa, Neja-Delta kan maganan Mamman Daura.

A hira da kungiyoyin su ka yi da jaridar a mabanbantan lokaci, sun nuna ba su goyon bayan kiran da Mamman Daura ya ke yi. Sai dai kungiyar ACF ta manyan Arewa ta ce dattijon ya yi gaskiya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, ya yi magana ta bakin hadiminsa, Emeka Attamah, ya na mai cewa akwai son rai a kalaman da ‘danuwan shugaban kasar ya yi.

Nnia Nwodo ya tunawa Mamman Daura cewa an fatattaki Goodluck Jonathan daga mulki a 2015 ne saboda mutanen yankin Arewa su na ganin cewa lokacinsu ne da za su yi mulkin kasar.

Hakazalika kungiyar matasan Ohanaeze ta bayyana cewa adalci da nuna daidaiton da shugaba Muhammadu Buhari zai iya yi kadai shine ya mika ragamar mulki hannun dan kabilar Igbo a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel