Jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari lokacin da ya ke kokarin tashi

Jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari lokacin da ya ke kokarin tashi

Wani karamin jirgin sama makare da hodar-Iblis ya yi hatsari ya yayin da ya ke kokarin tashi sama a hanyarsa ta zuwa kasar Australia a ranar Asabar kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Hatsarin jirgin saman ya tona asirin wasu masu safarar miyagun kwayoyi da ke Melbourne kuma an kama mutane biyar da ake zargin suna da alaka da masu safarar kwayoyi a Italiya.

Jirgin kirar Cesna wadda aka cika makil da kilogram 500 na hodar-iblis wato koken ya fado kasa ne yayin da ya ke yunkurin tashi daga wani karamin filin jirgi da ke Papua New Guinea a ranar 26 ga watan Yuli.

Jirgin sama makare da hodar Iblis ya yi hatsari lokacin da ya ke kokarin tashi
Jirgin sama makare da hodar Iblis ya yi hatsari lokacin da ya ke kokarin tashi. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Yan sandan Australia cikin sanarwar da suka fitar sun ce, "Akwai alamun hadama a cikin harkokin kungiyar ta masu safarar miyagun kwayoyin" inda suka ce bisa ga alamu nauyin hodar-iblis din ne ya hana jirgin tashi sama.

DUBA WANNAN: Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

An tuhumar mutum biyar din da aka kama a Queensland da Victoria da laifin hadin baki don safarar hodar Iblis kilogram 500 da wasu laifan daban masu alaka da safarar kwayoyin.

Za a iya yi wa kowannensu daurin rai da rai idan kotu ta same su da aikata laifin da ake tuhumarsu. An kama matukin jirgin bayan ya kai kansa wurin yan sanda.

Mahukunta sun ce jirgin ya taso ne daga wani karamin gari mai suna Mareeba da ke Papua New Guinea a arewacin Queensland amma ya yi lambo hukuma ba ta gan shi ba.

Daga bisani an gano hodar Iblis din da jirgin ya dako a ranar Juma'a bayan bincike a yankin. An kiyasta kudinsa zai kai Dallar kasar Australia miliyan 80 wanda ya yi daidai da Dallar Amurka miliyan 57.

Mutanen da aka kama masu shekaru 31, 36, 31, 33, da 61 duk ana tuhumarsu da laifuka daban daban. Mutum na farko ana tuhumarsa da safarar kwayoyi da almundanar kudi fiye da Dallar Australia Miliyan 1.

Yan sanda sun kuma kwace wasu kadarorinsa da kudinsu ya kai Dallar Australia Miliyan 3.5.

Wannan kamun da yan sandan suka yi na yana da cikin kamu mafi girma na muggan kwayoyi a tarihin kasar ta Australia. A shekarar 2016 an taba kama wata hodar-iblis din mai nauyin kilogram 500 a New South Wales.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel