Kawai ya Buhari ya mikawa dan kabilar Igbo mulki a 2023 - Ohanaeze

Kawai ya Buhari ya mikawa dan kabilar Igbo mulki a 2023 - Ohanaeze

Adalci da nuna daidaiton da shugaba Muhammadu Buhari zai iya yi kadai shine ya mika ragamar mulki hannun dan kabilar Igbo a 2023, kungiyar matasan Ohanaeze ta bayyana ranar Alhamis.

Yan kungiyar sun jaddada cewa yanzu ne karon yankin kudu maso gabas na gadan kujerar shugaban kasa.

A cewarsa, don nuna daidaito, tabbatar da zaman lafiya, da nuna adalci, ya kamata yan Najeriya, musamman yan Arewa su goyi bayan yan kabilar Igbo.

"Buhari ya mika mulki ga dan takaran Igbo a 2023. Ya bayyana karara yanzu ne karon yankin Kudu maso gabas a 2023." Dozie yace.

A cewarsa, muddin ba'a baiwa yankin Igbo shugabancin kasa ba, to ba'ayi adalci ba.

Kawai ya Buhari ya mikawa dan kabilar Igbo mulki a 2023 - Ohanaeze
Kawai ya Buhari ya mikawa dan kabilar Igbo mulki a 2023 - Ohanaeze
Asali: UGC

Hakazalika, shugaban Ohanaeze Ndigbo na jihar Anambara, Cif Damian Okeke-Ogene, ya jaddada cewa matsayarsa itace a baiwa kudu maso gabas gadon kujerar Buhari.

Dozie da Okeke-Ogene sun yi tsokaci ne kan jawabin da tsoWasu daga cikin kungiyoyin da ke kare mutanen Kudu da Arewacin Najeriya sun yi wa Mamman Daura raddi a game da maganar da ya yi na cewa cancanta zai yi aiki a zaben 2023.

Punch ta samu labari cewa kungiyoyi irinsu Middle Belt Forum, Ohanaeze Ndigbo, Afenifere da South-South Elders’ Forum ta mutanen Arewa, Ibo, Yarbawa, Neja-Delta sun yi magana.

A hira da kungiyoyin su ka yi da jaridar a mabanbantan lokaci, sun nuna ba su goyon bayan kiran da Mamman Daura ya ke yi. Sai dai kungiyar ACF ta manyan Arewa ta ce dattijon ya yi gaskiya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, ya yi magana ta bakin hadiminsa, Emeka Attamah, ya na mai cewa akwai son rai a kalaman da ‘danuwan shugaban kasar ya yi.

Nnia Nwodo ya tunawa Mamman Daura cewa an fatattaki Goodluck Jonathan daga mulki a 2015 ne saboda mutanen yankin Arewa su na ganin cewa lokacinsu ne da za su yi mulkin kasar.

hon sakataren kungiyar Arewa ACF, Anthony Sani, yayi cewa ba a baiwa shugaba Buhari mulki ba don yana dan Arewa.

Mallam Mamman Daura, babban aminin shugaba Buhari, ne ya fara magana kabilar da ya kamata a baiwa kujeran shugaban kasa.

A hirar da yayi da BBC Hausa, Mamman Daura ya ce bai kamata a yi amfani da yanki ko kabilar mutum don zabensi a 2023 ba. Kawai a duba cancanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel