'Yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna

Mutanen garin Udawa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna sun shiga ruɗani yayin da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kashe wani ɗan kasuwa a gonarsa.

An bayyana cewa sunan marigayin ɗan kasuwan Malam Jafaru Bello.

Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai masa hari ne a lokacin da ya tafi gonarsa a wani gari mai suna Goluwa a safiyar ranar Laraba.

An kuma gano cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu manoma uku daga gonarsa a ranan da suka kashe shi.

Yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna
Yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa a Kaduna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

Garin Udawa yana da iyaka da ƙaramar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Wani jagoran al'umma a garin, Malam Muhammadu Umaru wanda ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin ya ce wanda abin ya faru da shi makwabcinsa ne.

Malam Umaru ya ce, "Irin wannan abin bai taɓa faruwa ba; ta baya aka kashe shi. Makwogoronsa ne kawai ya rage da sun datse kansa. Jafaru makwabci na ne kuma ɗan kasuwa ne mai mata hudu da ƴaƴa 12.

Ƴan bindiga sun masa kisar rashin tausayi a gonarsa a safiyar ranar Laraba. Sun kuma sace wasu manoma uku sun tafi da su."

Ya ce ƴan bindigan su kan harbi waɗanda suka kama ne amma yanzu yankan rago suke musu wadda hakan ya jefa ƴan kauyen cikin damuwa.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar bai sama wayarsa ba.

Amma kwamishinan ƴan sandan jihar, CP, Umar Musa Muri ya ce ba zai iya tabbatar da afkuwar lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi.

Ƙaramar hukumar Chikun tana ɗaya daga cikin garuruwan da ake fama da matsalar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

A wani labarin, Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu a ranar Laraba ya kori ministan Iliminsa, David Mabumba a cewar fadar shugaban kasar bayan bidiyon tsiraicinsa ya bazu a kafafen sada zumunta.

Sanarwar daga fadar shugaban kasar ba ta fayyace dalilin korar ministan ba amma hakan ne zuwa ne bayan an saki bidiyon tsiraicin ministan a Twitter, Facebook da kuma Whatsapp.

Ta ce kawai Lungu "ya soke nadin da ya yi wa ministan ilimi ... nan take," kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An nada David Mabumba mai shekaru 49 a matsayin minista ne a gwamnatin Lungu a shekarar 2016.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel