Karin 'yan Najeriya 462 sun kamu da korona, jimilla 43,151

Karin 'yan Najeriya 462 sun kamu da korona, jimilla 43,151

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 462 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:37 na daren ranar Juma'a 31 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 462 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Korona ta sake harbin yan Najeriya 462, jimilla 42,689
Korona ta sake harbin yan Najeriya 462, jimilla 42,689
Asali: Twitter

FCT-93

Lagos-78

Plateau-64

Kaduna-54

Oyo-47

Ondo-32

Adamawa-23

DUBA WANNAN: Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

Bauchi-19

Rivers-9

Ogun-9

Delta-9

Edo-7

Kano-6

Enugu-6

Nasarawa-5

Osun-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Juma'a 31 ga Yulin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 43,151 .

An sallami mutum 19,565 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 879.

A wani rahoton, kunji cewa wasu gwamnatin jihohi sun haramta bukukuwan babbar sallah a lokacin da alummar musulmi ke shirin yin bikin babbar sallah wato Eid-el-Kabir na shekarar 2020.

Ga dai jerin jihohin da suka saka dokokin haramta bukukuwar Sallah a bana domin dakile yaduwar annobar coronavirus kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

1. Jihar Kano

2. Jihar Plateau

3. Birnin Tarayya Abuja

4. Jihar Osun

5. Jihar Niger

6. Jihar Kwara

7. Jihar Jigawa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel