Buhari ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa yan Najeriya - Gwamna Bagudu

Buhari ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa yan Najeriya - Gwamna Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiu Bagudu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawuran da ya yiwa yan Najeriya lokacin da yake yakin neman zabe a 2015.

Gwamna ya bayyana hakan a jawbain Sallan da yayi ranar Juma'a a Birnin Kebbi, inda yace lamarin tsaro ya fi kyau yanzu fiye da lokacin da ya hau ragamar mulki.

Kan lamarin yaki da rashawa kuwa, ya ce Najeriya ta samu nasara wajen dakile masu cin hanci da rashawa.

Bagudu ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan irin amincewar da yake da dan jihar Kebbi, wanda yake ministan shari'a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami.

Yace: "A kan lamarin tsaro, jami'an tsaro na iyakan kokarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana."

"A yanzu, babu yankin kasar nan dake karkashin yan ta'adda kamar yadda yake a baya."

"Buhari ya samu nasaran inganta tattalin arzikin kasa, kamar yadda yayi alkawari."

"Buhari ya samu nasarar cika sukkan alkawura uku da yayi lokacin da yake yakin neman zabe a 2015."

KU KARANTA: Hanyoyi hudu da za a iya amfani da su don adana naman sallah

Buhari ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa yan Najeriya - Gwamna Bagudu
Buhari ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa yan Najeriya - Gwamna Bagudu
Asali: Twitter

hugaba Muhammadu Buhari ya ce yan Najeriya sun san gwamnatinsa ta yi iyakan kokarinta wajen shawo kan matsalan tsaro da ake fama da shi a fadin tarayya.

Yayinda yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan Sallar Idi a fadar shugaban kasa Aso Villa, shugaban kasan yace ba lokacinsa aka fara fuskantar matsalar tsaro ba.

Amma ya nuna bacin ransa kan gazawan hukumomin tsaro , inda yace ya kamata a ce sun fi hakan kokari, The Cable ta ruwaito.

Yace: "Ina son yan Najeriya su farga kan kasarsu kuma su san abinda muka gada lokacin da muka dau mulki a 2015 Boko Haram ne a Arewa maso gabas sannan barandanci a Kudu maso kudu.... Yan Najeriya sun san munyi iyakan kokarinsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel