Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sallar Idi Eid El-Kabir tare da iyalansa da wasu hadimansa a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaban kasar ya ce ya yi hakan ne domin bin shawarwarin kwamitinsa ta yaki da Covid 19, PTF, da kuma kwamitin koli da harkokin addinin musulunci (NSCIA).

Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja
Shugaba Buhari da iyalansa. Hoto daga Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja
Shugaba Buhari yayin gudanar da sallar Idi. Hoto daga Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya yi amfani da shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, ya taya alumma murnar bikin sallar:

"Na yi Sallar Idi a gida tare da iyalai na a safiyar yau bisa shawarwarin kwamitin shugaban kasa ta yaki da Covid 19, PTF, da kuma kwamitin koli da harkokin addinin musulunci (NSCIA). Ina taya mu murnar Sallar baki daya."

DUBA WANNAN: Coronavirus ta sake harbin yan Najeriya 481 yau, jimilla 42,689

Limamin masallacin gidan gwamnati, Abdulwaheed Suleiman ne ya jagorancin sallar ta rakaa biyu.

An yanka manyan raguna biyu kamar yadda ya ke a sunnar babbar sallah domin yin shagali.

Bayan hakan, Shugaban kasar da iyalansa sun dauki hotuna wadda daga bisani aka wallafa su dandalin sada zumunta.

A ranar Laraba, hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ya ce shugaban kasar ba zai karbi gasuwar sallah ba daga malaman addini, yan siyasa, shugabanin gwamnati ko mutanen gari don dakile yaduwar korona.

Shugaban kasar ya yi wa musulmi fatan yin bukukuwan sallah cikin zaman lafiya tare da shawartar su da su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya da kwamitin shugaban kasar ta yaki da annobar ta bayar.

"Idan mutane marasa yawa za su yi sallar Idi tare, su saka takunkumin fuska, sannan su bayar da tazara.

"Ana bayar da shawarar ayi sallar a fili sannan ana shawartar masallata su tafi filin sallar da dadduma ko taburmarsu," a cewar sanarwar.

Buhari ya kuma shawarci mutane su bi dokokin da jihohi da kananan hukumominsu suka saka sannan ya sake yi wa alummar fatan alheri yayin da suke bikin sallar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel