Coronavirus ta sake harbin yan Najeriya 481 yau, jimilla 42,689
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 481 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:33 na daren ranar Alhamis 30 ga Yulin shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 481 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: Twitter
FCT-96
Lagos-89
Plateau-68
Ogun-49
Edo-44
DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba
Rivers-43
Oyo-25
Osun-23
Delta-15
Enugu-11
Kano-7
Kaduna-7
Bauchi-2
Bayelsa-1
Yobe-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Alhamis 30 ga Yulin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 42,689.
An sallami mutum 19,270 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 878.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng