Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo)

Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo)

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Laraba ya nuna bacin ransa a kan yanayin aikin dakarun sojin da ke kokarin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.

Ya nuna fushinsa a kan harin da wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne suka kai masa a hanyarsa ta fita Baga.

Baga gari ne da ke da nisan a kalla kilomita 196 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnan ya matukar fusata da lamarin, ganin cewa akwai dakarun sojin masu tarin yawa a nisan da bai wuce mil 4 ba wanda daidai yake da kilomita 4 daga Baga, amma basu iya kwace garin ba.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sake bude babbar hanyar Monguno zuwa Baga ga ababen hawa wacce aka yi shekaru biyu da rufewa.

"Sama da shekara daya kuna nan, akwai soji 1,181 a nan. Idan ba za ku iya karbar Baga ba wacce take da nisan da bai kai kilomita biyar ba daga inda kuke, toh me kuke yi?

Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo)
Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo). Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda dan sanda ya dinga lalata da ni tun dare har asuba - Matar da ta take doka

"Ina tunanin kawai mu hakura da Baga ko? Zan sanar da shugaban dakarun sojin da ya kwasheku ya kaiku inda za ku yi amfani.

"Kun ce babu Boko Haram a nan, toh su waye suka kawo mana farmaki? Ina tantama idan aka ce babu Boko Haram a nan garin," gwamna Zulum ya tambaya.

Wasu wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai wa tawagar gwamnan hari a garin Baga a ranar Laraba.

Ya jagoranci daruruwan jama'ar Kukawa, Cross da Baga zuwa tsohon garinsu bayan shekaru biyu da 'yan ta'addan suka kwace garin.

Tun farko, kwamandan Operation Lafiya Dole da ke Baga, Birgediya Janar Garba, ya tabbatar wa da Zulum da tawagarsa cewa babu 'yan ta'addan Boko Haram a garin.

Gwamnan wanda ya je zagayawa, ya koma Maiduguri lafiya. Kafin ya bar Monguno zuwa Baga, Zulum ya gabatar da motocin sintiri 12 ga dakarun sojin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel