'Yan bindiga sun kai wa tawagar gwamnan Borno hari

'Yan bindiga sun kai wa tawagar gwamnan Borno hari

An kai wa tawagar gwamna Babagana Zulum na jihar Borno hari a garin Baga da ke jihar Borno a ranar Laraba 29 ga watan Yulin shekarar 2020.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa The Cable cewa gwamnan yana kan hanyarsa ta zuwa sansanin yan gudun hijira da ke jihar ne a lokacin da abin ya faru.

"Gwamnan ya tafi Kukawa, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Baga ne aka kai masa hari. Babu wanda ya jikkata," a cewar majiyar.

Yan bindiga sun kai wa tawagar gwamnan Borno hari
Yan bindiga sun kai wa tawagar gwamnan Borno hari. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba

A halin yanzu dai ba a tabbatar ko 'yan kungiyar ta'adanci ta Boko Haram ne suka kai harin ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa Zulum ya koma Maiduguri, babban birnin jihar misalin karfe 9.10 na daren ranar Laraba.

Wani Mohammed Mai Bukar, daya daga cikin hadiman gwamnan ya tabbatar wa alummar garin cewa babu abinda ya sami gwamnan.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bukar ya rubuta, "Ga mazauna jiharmu, Mai girma Farfesa Zulum da tawagarsa suna nan lafiya kuma babu wanda ya mutu. Mun gode."

Wannan shine karo na biyu da ake kai wa tawagar Gwamna Zulum hari cikin shekara guda.

A yayin da gwamnan ke dawowa daga wata tafiya daga karamar hukumar Baga a bara, an kai wa tawagarsa hari a Konduga duk dai a jihar ta Borno.

Harin ya faru ne watanni bakwai bayan da yan taada suka kai wa tawagar Kashim Shettima tsohon gwamnan jihar hari a hanyarsa ta zuwa Gamboru Ngala duk dai a jihar Borno.

A kalla mutane 60 suka riga mu gidan gaskiya a wancan harin kuma aka sace kimanin mutane 100.

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau da Kwamishinan Labarai na jihar Borno, Babakura Abba-Jatto don karin bayani amma ba su amsa sakon kar ta kwana ba kuma ba su daga wayarsu ba.

Ku saurari karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel