Hotuna: Al'ummar musulmi sun fara aikin hajji duk da annobar korona
Mahajjata sanye da takunkumin fuska sun fara aikin hajjin bana a ranar Laraba sai dai adadin su ba shi da yawa sakamakon annobar korona da ta tilastawa Saudiyya takaita adadin mahajjatan.
Hajji dai yana daya daga cikin shika shikan addinin musulunci da duk musulmin da Allah ya bawa iko ake son ya yi a kalla sau daya a rayuwarsa.
A sauran shekaru, ana iya cewa hajji na daya daga cikin taron addini da ke samun hallartar mutane da dama a duniya amma a bana lamarin ya canja.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Kimamin mutum 10,000 wanda dama mazauna kasar Saudiyya ne aka bawa ikon hallartar ibadar da aikin hajji a maimakon kimanin mutum miliyan 2.5 da suka yi aikin hajjin a bara.
DUBA WANNAN: Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba
Musulmi sun isa masallacin haramin na Makka inda suka fara gudanar da dawafin na zagaye masallacin haramin suna adduoi kamar yadda wasu faya fayen bidiyo na kasar Saudiyya suka nuna.
An yi wa mahajjatan gwajin zazabi sannan an killace su na kwanaki 14 a lokacin da suka isa kasar mai tsarki a karshen makon da ta gabata. Anyi hakan ne don tantance masu dauke da cutar korona.

Asali: Twitter
Kafafen watsa labarai na Saudiyya ya nuna yadda ake yi wa jakkunan mahajjata feshin maganin kashe kwayoyin cutar kuma wasu daga cikinsu an basu wani naura sun saka a hannunsu domin a rika sanin inda suke a kowanne lokaci.
Mahukunta a kasar ta Saudiyya sun zagaye dakin na Kaaba a bana inda suka ce ba za a bari mahajjata su rika shafansa ba domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
An kuma kara adadin asibitoci da asibitocin tafi da gidanka da motoccin daukan marasa lafiya a Makka domin kula da lafiyan cikin mahajjatan cikin idan bukatar hakan ta taso.
"Ba bu wata fargabar tsaro game a aikin hajjin amma an takaita adadin mahajjatan ne kawai domin dakile yaduwar annobar coronavirus," a cewar direktan tsaron alumma na Saudiyya, Khalid bin Qarar Al-Harbi.
An kuma hana kafafen watsa labarai na kasashen duniya damar zuwa daukan rahotanni yayin aikin hajjin na bana a yunkurin da gwamnatin kasar ta yi na tsaurara matakan tsaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng