Ina jin dadin kasancewata shugaban kasa yayin da rayuwar 'yan Najeriya ta inganta - Buhari

Ina jin dadin kasancewata shugaban kasa yayin da rayuwar 'yan Najeriya ta inganta - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi matukar farin ciki kasancewarsa mai rike da akalar iko ta kasar yayin da rayuwar al'ummar Najeriya ta inganta.

Yayin wata hira da ya yi da Mujallar The Signature 50, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa a koda yaushe tana ci gaba da jajircewa domin ganin rayuwar 'yan Najeriya ta inganta fiye da duk wata kimantawa.

"An dauke mu a matsayin masu mafi girman tattalin arziki a Afirka ta fuskoki daban-daban. Ta yaya hakan zai farantawa mutum a matsayinsa na Shugaban Najeriya? Tabbas, mutum zai ji daɗi. Amma hakan kadai bai wadatar ba," in ji shugaban.

"Zan fi jin dadi sosai idan muka wuce kimantawa ko wata ƙididdiga kadai, a yayin da ya kasance mafi akasarin 'yan Najeriya sun fara jin tasirin wannan kyakkayawar kima."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

"Lokacin da 'yan Najeriya suka yi zurfi cikin annashuwa da jin dadi, idan rayuwarsu ta inganta sosai kuma tasirin matsayinmu na masu mafi girman tattalin arziki ya nuna aljihunan su, to zan yi farin ciki sosai."

Da yake tsokaci kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun daga hawansa mulki zuwa yanzu, Buhari ya ce tattalin arzikin kasar nan ba ya cikin irin mummunan yanayin da ya tsince sa.

Da yake bayanin cewa duk da ci gaban da ake samu ba shi da hanzari kamar yadda yake muradi, Buhari ya ce wadatar da aka samu zuwa yanzu ta ba da kwarin gwiwa cewa abubuwa suna ta tafiya daidai.

A cewar shugaban, hangen nesan da ya ke yiwa Najeriya shine tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar ya bunkasa ta hanyar samun gagarumin ginshiki da tubalin da babu abinda zai girgiza shi koda an samu janyewar danyen man fetur.

Buhari ya ce hanyar ci gaba da Najeriya ta dauko yana kamanceceniya da irin tafarkin da kasar China ta ratsa kuma ta samu nasara.

KARANTA KUMA: Lakcarori, ma'aikatan gwamnatin tarayya da na jiha na zambatar aikin N-Power

"Dalilin haka ya sanya muka jajirce wajen inganta dangartakar da ke tsakaninmu da kasar China, wadda a kullum ta ke ci gaba da bunkasa ta hanyar duk wata dama da muka samu," inji shugaban kasar.

"Tun daga horo, hadin kan kasa, mayar da hankali kan kimiyya da fasaha, manufofin talakawa da sauran su, kasar China ta zama daya daga cikin manyan kasashe mafi karfin tattalin arziki a duk duniya, kuma ta taka wannan munzali ne cikin shekaru arba'in."

Akwai izina da ya kamata mu dauka kuma Najeriya tana da abubuwa da dama da za ta koya daga kasar China kuma a ƙarshe mu ci riba mai girman gaske."

A ƙarshe shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin sa za ta yi iyaka bakin kokarin ta domin ganin ta rage radadin da annobar korona da kuma dakile tasirin da ta yi a kan 'yan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng