Buhari ya naɗa mataimakan kwamishina 2 a hukumar NAICOM

Buhari ya naɗa mataimakan kwamishina 2 a hukumar NAICOM

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake yin wasu sabbin naɗe-naɗen mukamai biyu a gwamnatinsa.

Shugaban kasa Buhari ya amince da naɗin Alhaji Sabi'u Abubakar da kuma Mista Oba Olaniyi, a matsayin sabbin mataimakan kwamishina a Hukumar Inshora ta NAICOM.

Bayanin amincewa da naɗin na kunshe ne a cikin sanarwar da Mista Rasaaq Salaami, babban kwamishinan NAICOM ya fitar a ranar Litinin yayin zantawa da manema labarai a Abuja.

Salami ya bayyana cewa, Alhaji Abubakar zai kasance mataimakin kwamishina mai kula da tsare-tsare a hukumar yayin da Oluniyi zai kasance mataimakin kwamishina mai kula da harkokin gudanarwa.

Haka kuma sanarwa ta kuma ce, nadin ya fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Yuli za kuma su kasance a kan mukamin har zuwa shekara 5 masu zuwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zauren babban dakin taro na Council Chambers
Hoto daga fadar shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zauren babban dakin taro na Council Chambers Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sanarwar ta kuma yi bayanin cewa, za a fara lissafin tasirin naɗin mukamin tun daga ranar 17 ga watan Yuli, har zuwa nan da shekaru biyar masu zuwa.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2020, shugaba Buhari ya sa sunayen tashoshin jirgin kasa bayan wasu ‘yan Najeriya da su ka cancanta da karramawa.

A cikin wannan jerin manyan kasa da aka karrama, mace guda kacal aka samu. Wannan mace kuwa ita ce Funmilayo Ransome-Kuti wanda aka fi sani da Funmilayo Anikulapo-Kuti.

KARANTA KUMA: Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 40,000 - NCDC

Madam Funmilayo Anikulapo-Kuti MON ta rasu ne a 1978 ta na mai shekara kusan 78 da haihuwa. Marigayiyar ita ce macen farko da ta halarci makarantar Abeokuta Grammar School.

Funmilayo Anikulapo-Kuti ta yi karatu a Ogun da kasar Ingila, ta kuma yi aiki a matsayin malamar makaranta, sannan ta yi gwagwarmaya wajen karbowa mata hakki a lokacinta.

Daga cikin ‘ya ‘yanta akwai shararren mawakin nan Fela Kuti, da kuma Beko Ransome-Kuti. Sauran ‘ya ‘yanta su ne: Olikoye Ransome-Kuti, da Dolupo Ransome-Kuti.

Mutane 23 shugaban kasa Buhari ya karrama, daga cikinsu akwai tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan; jagoran APC, Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

A jerin akwai karin wasu tsofaffin gwamnan Legas Babatunde Fashola da Lateef Jakande. Farfesa Wole Soyinka da tsohon mataimakin shugaban kasa, Dr. Alex Ekwueme.

An ruwaito cewa karancin matan da aka samu bai yi wa jama’a dadi ba. Wasu sun yi tunanin za a karrama irinsu Dr Stella Adadevoh wanda ta mutu wajen yaki da cutar Ebola a 2014.

Sanata Shehu Sani ya bada shawarar a sa sunan tashar jirgin Kaduna bayan Tolulope Arotile, macen da ta zama matukiyar jirgin yakin farko a cikin sojoji wanda ta mutu kwanaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel