An kashe shugaban ƴan bindiga ‘Dangote’ yayin sumamen da sojoji suka kai a Zamfara (Bidiyo)

An kashe shugaban ƴan bindiga ‘Dangote’ yayin sumamen da sojoji suka kai a Zamfara (Bidiyo)

Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce ta kashe daya daga cikin shugabannin ƴan bindiga da ke adabi Arewa Maso Yamma, mai suna ‘Dangote’ yayin wani hari da sojojin sama suka kai wa ƴan fashin Zamfara.

Kakakin sojin, John Enenche ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce rundunar musamman ta Operation Hadarin Daji ta tarwatsa mafakar ƴan bindigan a Dajin Doumborou a Zamfara.

"Harin da rundunar Operation Hadarin Daji ta kai ya haifar da kyakkyawan sakamako ta hanyar tarwatsa sabon sansanin ƴan bindiga ƙarƙashin jagorancin 'Dangote,'" in ji sanarwar.

An kashe ‘Dangote’ da wasu ƴan bindiga yayin sumamen da sojoji suka kai a Zamfara
An kashe ‘Dangote’ da wasu ƴan bindiga yayin sumamen da sojoji suka kai a Zamfara. Hoto da Rundunar Soji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP

Enenche ya ce hare haren da dakarun sojan saman Najeriya suka kai a ranar Alhamis ya yi sanadin mutuwar yan bindiga masu yawa.

Ya ce an kai harin ne bayan samun bayannan sirri da suka tabbatar da cewa yan bindigan sun kafa sabuwar sansani a kusa da wani dutse da ke dajin.

Kakakin sojin ya kara da cewa yan bindigan suna kai kayayyakin zirga zirgan su da suka hada da babura da dabobi da dama da suka sace a hannun mutane zuwa sabon sansanin.

"Jiragen da suka kai harin sun yi luguden wuta a sansanin inda suka tarwatsa yan taadan tare da kashe wasu daga cikinsu.

"An hangi wasu dama suna kokarin tserewa daga wurin suma aka bi ta kansu aka halaka su da luguden wuta.

"Shugaban hafson sojojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya yabawa mayakan rundunar ta muamman na Operation Hadarin Daji saboda kwarewarsu wurin aiki.

"Ya bukaci su cigaba da jajircewa wurin kai hare haren na sama yayin da suka bawa sojojin kasa gudunmawa domin ganin bayan dukkan yan bindigan," in ji shi.

Kakakin rundunar sojin bai fadi adadin yan bindigan da aka kashe ba kuma bai ambaci ko an samu wadanda suka jikatta ko suka mutu ba a bangaren sojojin yayin harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel