Kwastam ta kori jami'inta da Buhari ya karrama saboda ƙin karɓar rashawar N180m

Kwastam ta kori jami'inta da Buhari ya karrama saboda ƙin karɓar rashawar N180m

- Hukumar Kwastam ta kori jamiinta da ya yi fice wurin yaki da cin hanci da rashawa, Bashir Abubakar

- Ta kuma sallami wani jamiinta mai mukamakin mataimakin shugaba mai suna Aminu Dahiru

- Sanarwar da Kakakin hukumar ya fitar ta ce an kore su daga aiki ne bayan samunsu da sakaci

Hukumar Hana Fasakwabri, Kwastam, a ranar Laraba ta sanar da korar jami’inta, mataimakin shugaba (ACG) Aminu Dahiru da kuma tilasta wa wani jami’in, ACG Bashir Abubakar yin murabus.

ACG Bashir Abubakar dai shine jami'in da Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama da lambar girmamawa shekarar 2019 saboda kin karbar toshiyar baki na Dalar Amurka 412,000 kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

An sallami jami’in kwastan da ya ki karbar rashawar miliyan N180
An sallami jami’in kwastan da ya ki karbar rashawar miliyan N180. Hoto daga The Source NG
Asali: Twitter

Sanarwar da kakakin hukumar, Joseph Attah ya fitar a madadin Shugabanta, Hamid Ali ta ce mambobin kwamitin zartarwa na hukumar sun amince da wannan matakin da ya dace da tsarin yi wa hukumar garambawul.

An kori jamian biyu, Abubakar da Dahiru ne bayan samun su da laifin sakaci a watan da ya gabata kamar yadda binciken da kwamitin ladabtarwa da aka kafa ya bayyana.

An tuhumi ACG Aminu Dahiru da hannu a badakalar fasakwabrin manyan motoci guda 295 dauke da man fetur a watan Disambar 2019 lokacin yana aiki da Rundunar Kare kan Iyakokin kan Tudu na Kasa.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace sufetan 'yan sada da wasu mutum 5 a Adamawa

Shi kuma ACG Bashir Abubakar ana zarginsa da bayar da umarnin yin samame a rumbun ajiyar shinkafa ‘yar gida a kokarinsa na gano shinkafar waje a rumbunan ajiyar wani fitaccen mutum a garin Daura da ke Jihar Katsina.

A watan Nuwamban 2019, Shugaba Buhari da Shugaban Hukumar Kwastam, Hamid Ali suka karrama Bashir Abubakar da lambar yabo bisa gaskiyarsa da jajircewa wurin aiki.

Bashir Abubakar ya kuma samu yabo daga hukumar a shekarar 2018 bayan da yaƙi karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 412,000 daga hannun wasu da suka shigo da haramtattun kwayoyin Tramadol lokacin yana kula da rundunar a shiyar Apapa a Legas, lamarin da ya sa ya yi fice.

Har wa yau, Sanarwar ta ce rundunar ta yi wa wasu jamianta 2,634 karin girma tare da tabbatar da naɗin masu taimakawa shugaban rundunar guda biyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel