Tsohon Kakakin Majalisa, Yakubu Dogara ya dawo APC
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Yakubu Dogara ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya koma APC.
Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya tabbatar da hakan bayan ganawar da suka yi da Shugaba Buhari a yau Juma'a a Abuja.
Buni, yayin amsa tambayoyin manema labarai ya ce, "Bai kamata ƴan Najeriya su yi mamaki ba saboda dama tsohon Kakakin ɗan APC ne. Dalilin da yasa ya bar APC ta gushe."
Dogara ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne a ranar 29 ga watan Janairun 2019.
Ya koma PDP ya kuma samu tikitin takarar kujerar Majalisar wakilai na yankin Bigire/Dassa/Tafawa Balewa na jihar Bauchi tun kafin ya sanar da komawarsa.
Da aka tambaye shi ko Dogara ya koma APC, Shugaban kwamitin rikon na APC ya sama da cewa, "Eh, ya dawo."
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta nemi Buhari ya yi murabus, ta bayar da dalili
An tambayi Buni ko dawowar Dogara APC na da alaƙa da zaɓen 2023, ya ce, "Eh, ba ma shirin zaɓen 2023 ba, muna saita jam'iyyar ne ta yadda ko bayan mu za ta cigaba da bunƙasa.
"Ba batun yanzu kawai ake ba ko wani ƙanƙanin lokaci, ba maganan zaɓe bane ko yaƙin neman zabe, magana ce ta gina jam'iyya."
Shugaban riƙon na APC da ya ke magana kan ƙoƙarin da suke na zawarcin tsaffin ƴan jam'iyyar ya ce, "Muna ganawa da tsaffin ƴan jam'iyyar mu musamman waɗanda ke da niyyar dawowa. Muna maraba da su. Muna tabbatar musu zamu yi musu adalci.
"Za mu yi wa dukkan mambobin mu adalci don hakan ne zai haifar da zaman lafiya, hakan zai sa jam'iyya ta ƙarfafa da kuma gina ta. Idan babu adalci, hakan ba zai yi su ba kuma muna da tabbacin zamu yi wa kowa adalci."
Buni ya ce ya ziyarci shugaban kasa ne kan batun ƙoƙarin da su ke yi na gina jam'iyya kuma "ya sanar da shi cigaban da ake samu."
Da ya ke tsokaci kan yadda shugaban kasa ya karbi labarin, ya ce, "Ya yi maraba da shi. Ya yi murna da abinda ya faru. Muna gina jam'iyya kuma hakan na cikin matakan da muke ɗauka na gina jam'iyyar."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
dan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng