Shugaba Buhari ya sabunta naɗin Joseph Ari a matsayin shugaban ITF

Shugaba Buhari ya sabunta naɗin Joseph Ari a matsayin shugaban ITF

- An sake yin wani babban nadi a bangaren kasuwanci da cinikayya

- An sake naɗa Me Joseph Ari a matsayin shugaban hukumar ITF

- Naɗin zai fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Satumban 2020 zuwa shekara hudu gaba

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sake naɗa Joseph Ari a matsayin shugaban Asusun Koyar da Ayyuka (ITF) na tsawon shekaru huɗu.

Shugaban kasar ya amince da nadin ne cikin wasikar da ya aike wa Ma'aikatar Cinikayya da Saka Hannun Jari a ranar Talata 16 ga watan Yulin 2020.

Shugaba Buhari ya sabunta nadin Joseph Ari a matsayin shugaban ITF
Shugaba Buhari ya sabunta nadin Joseph Ari a matsayin shugaban ITF
Asali: UGC

An fara naɗa Ari a matsayin shugaban ITF ne a shekarar 2016 kuma naɗinsa na biyu zai fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Satumban 2020.

Har wa yau, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaba Buhari ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasikar amincewa da nadin Lamido Yuguda a matsayin sabon shugaban SEC.

DUBA WANNAN: Alkali ya raba aure saboda mata ta ce mijin “ɗan ƙarya ne”

Shuagaban Majalisa, Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan yayin da ya ke karonto wasikar nadin Yuguda a zaman majalisar na ranar Talata 18 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari kuma ya nemi a tabbatar da naɗin mutum uku; Reginald C. Karausa, Ibrahim D. Biyu da Obi Joseph a matsayin kwamishinonin hukumar.

"Kamar yadda sashi na 3 da 5(1) na Investment and Securities Act 2007 ya tanada, ina neman majalisar ta tabbatar da naɗin waɗanda aka zaɓa a matsayin shugaba da kwamishinonin SEC," a cewar wasikar.

A wani labari mai kama da wannan, Shugaba Buhari ya amince da nadin Kashim Ibrahim-Imam a matsayin shugaban Asusun Ilimin Makarantun Gaba da Sakandare (TETFUND).

Ibrahim-Imam fitaccen ɗan siyasa ne a kasar kuma shine ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Borno a 2003 da 2007.

Labarin nadinsa na dauke cikin wasika mai kwanan watan 14 ga watan Mayu da ministan Ilimi Adamu Adamu ya aike masa.

An nada shi na wa'adin shekaru hudu ne inda za a iya sabunta naɗin idan an gamsu da aikinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel