Kano ce kan gaba wurin gwajin cutar Korona - NCDC

Kano ce kan gaba wurin gwajin cutar Korona - NCDC

- Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta jinjina wa jihar Kano kan yaƙi da cutar Covid-19

- Shugaban Hukumar, Chikwe Ihekweazu ne ya yi wannan yabon inda yace Kano ce kan gaba wurin gwaji

- Dr Ihekweazu ya shawarci sauran jihohi Najeriya su yi koyi da Kano a wannan yawaita gwajin kwayar cutar ta korona

Hukumar Kiyaye Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC, ta yabawa jihar Kano saboda zama zakara wurin gwajin korona a ƙasa baki ɗaya.

"Kano tana yi gwaji fiye da ko wane jiha a Nijeriya," a cewar shugaban NCDC, Dr Choker Ihekweazu.

Shugaban na NCDC na ƙasa ya yabawa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje saboda jajircewarsa wurin yaƙi da annobar ta Covid-19.

Kano ce kan gaba wurin gwajin cutar Korona - NDDC
Kano ce kan gaba wurin gwajin cutar Korona - NDDC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Alkali ya raba aure saboda mata ta ce mijin “ɗan ƙarya ne”

Sanarwar ta babban sakataren watsa labarai na gwamnan Abba Anwar ta ce Shugaban na NCDC ya bukaci sauran jihohi suyi koyi da jihar ta Kano.

Ihekweazu ya lura cewa a halin yanzu ba a samun yaduwar cutar kamar yadda ake samu a baya kuma ya gamsu da halin da jihar ke ciki a yanzu.

An gano cewa gwamnatin jihar Kano ta yi farin ciki da wannan yabon da NCDC ta yi mata.

"Wannan jinjinar za ta ƙara wa gwamnan da al'ummar jihar ƙwarin gwiwa su ƙara jajircewa wurin yaƙi da coronavirus," kamar yadda wani jami'in gwamnati ya shaidawa The Nation.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya na jihar Legas, ya ce gwamnati na kashe kimanin N500,000 zuwa Naira miliyan 1 kan kowanne mai cutar korona a jihar idan ta tsananta.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Abayomi ya ce yawan kudin da ake kashewa majinyatan cutar ya danganta ne da tsananin da cutar ta yi.

Kwamishinan ya ce suna kashe kusan N100,000 ga majinyacin cutar da bata yi wa tsananin kamu ba.

"Domin maganin cutar ga wanda bata tsananta ba ko take tsaka-tsakiya a cibiyar killacewa, muna kashe N100,000 a rana daya," Abayomi yace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel