Maganin Madagascar baya warkar da cutar COVID-19 - Gwamnatin tarayya

Maganin Madagascar baya warkar da cutar COVID-19 - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta ce maganin gargajiya da kasar Madagascar ta samar baya maganin cutar COVID-19

- Ministan kiwon lafiya Dr. Osagie Ehanire, ya ce sinadarin da aka hada maganin iri daya ne da sinadaran Tazargade

- Ministan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun yawaitar masu dauke da cutar a kowacce rana

A ranar Alhamis, gwamnatin Nigeria ta bayyana cewa maganin gargajiya da kasar Madagascar ta sarrafa ba ya wani tasiri akan cutar COVID-19 sabanin yadda ake kuranta shi.

Ministan kiwon lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a Abuja a bitar da kwamitin dakile yaduwar Coronavirus take yiwa shugaban kasa kan halin da ake ciki.

A cewarsa, cibiyar bincike da bukasa magunguna ta Nigeria (NIPRD) ta fitar da rahotonta na mkarshe kan maganin gargajiya da kasar Madagascar ta samar.

Kuma rahoton ya bayyana cewa sinadaran da aka hada maganin iri daya ne da sinadaran da ke cikin itaciyar Tazargade.

"A lokacin da aka yi bincike, an ga cewar yawan shan maganin na rage tari, amma bai buna cewar yana maganin cutar COVID-19 kamar yadda ake shelantawa ba.

"Sai dai, zamu ci gaba da zage damtse wajen bin hanyoyi na gano maganin cutar Coronavirus," a cewar Ehanire.

Ministan ya ce yawaitar sabbin masu dauke da cutar da ake samu a makonnan ya haura daga 500 zuwa 700, inda awanni 24 da suka wuce aka samu sabbin mutane 543 dauke da cutar.

KARANTA WANNAN: Babu wanda ya isa ya hana Tinubu zama shugaban Nigeria a 2023 - Kungiyar Arewa

Maganin Madagascar baya warkar da cutar COVID-19 - Gwamnatin tarayya
Maganin Madagascar baya warkar da cutar COVID-19 - Gwamnatin tarayya
Asali: UGC

A halin yanzu, mutane 38,344 ne ke dauke da cutar COVID-19 a Nigeria, inda kuma mutane 15,815 suka warke daga cutar bayan da akayi masu magani har aka sallamesu.

"A wannan halin, mun rasa mutane 813, inda muka tattara alkaluman mutanen da aka yiwa gwajin gaba daya zuwa 247,825."

"Bisa ga karuwar mutanen da muke samu, zamu iya cewa, akwai masu dauke da cutar da yawa a cikin al'umma, kenan, akwai yiyuwa karuwar wadanda zasu kamu," a cewar Ministan.

Sai dai ya jinjinawa jajurtattun 'yan Nigeria, wadanda aka gwadasu kuma aka same da cutar amma suka fito suka bayyanawa jama'a domin dakile yaduwar cutar.

Ya ce wadanda suka damu da kasar ne suka fito suka nunawa duniya cewa ba abun kunya bane ko abun boyewa don ka kamu da COVID-19, kuma sun nuna yardarsu ga kiwon lafiya na kasar.

A yayin da yake jinjinawa ma'aikatan kiwon lafiya na kasar, ministan ya kuma ce har yanzu an mayar da hankali kan dakile yaduwar cutar ne kawai, wanda yafi magani.

Ehanire ya ce ma'aikatar kiwon lafiya ta hannun hukumar da ke yaki don dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC sun samar da cibiyoyin gwajin Coronavirus 59 a fadin ksar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng