Buhari zai tafi Mali a ranar Alhamis

Buhari zai tafi Mali a ranar Alhamis

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai bar birnin tarayya Abuja zuwa Bamako a Jamhuriyar Mali don kai ziyarar aiki ta kwana daya kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

Ziyarar da Buhari zai kai Mali za ta zama karo na farko da Shugaban Kasar zai fita daga kasar tun bayan bullar annobar coronavirus da ta karade duniya.

Sanarwar da mai taimakawa shugaban kasa na musamman a fanin watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ta ce an shirya tafiyar ne bayan da wakilin ECOWAS na musamman a Mali, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Buhari.

Buhari zai tafi Mali a ranar Alhamis
Buhari zai tafi Mali a ranar Alhamis. Hoto daga This Day
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce Buhari da wasu shugabannin ECOWAS karkashin jagorancin shugaban Jamhuriyar Nijar, Issoufou Mahamadou sun shirya yin taro a Mali domin cigaba da tattaunawa kan yadda za a wareware rikicin da ke adabar kasar.

DUBA WANNAN: Neman sauke hafsoshin tsaro: Buhari ya 'watsa wa ƴan majalisa kasa a ido'

Shugaba mai masaukin baki, Ibrahim Boubacar Keita da shugabannin kasashen Senagal, Machy Sall, Nana Akufo-Addo na Ghana da Alassane Ouattara of Cote d’Ivoire suma za su hallarci taron.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Buhari tare da Mr Jean-Claude Kassi Brou a ranar Talata ne don yi wa Shugaba Buhari bayanin abinda ke faruwa a Mali haka ya saka shugabannin na ECOWAS suka yanke shawarar yin taron.

"Za mu tambayi shugaban Nijar, wanda kuma shine shugaban ECOWAS ya yi mana bayani daga nan kuma za mu san matakin da zamu dauka, " a cewar Shugaba Buhari.

Ya mika godiyarsa da Dr Jonathan bisa kyakyawan bayanin da ya yi masa a kan lamarin na Mali "da ka dade kana lura da shi tun lokacin kana shugaban kasar Najeriya."

Tsohon shugaban kasar ya yi wa Buhari bayani a kan abubuwan da ke faruwa a matsayinsa na jakada na musamman domin samar da zaman lafiya a Mali da wasu yan kasar ke zanga zangar sai Shugaba Keita ya sauka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel