Majalisar Dattawa ta bukaci Buratai da sauran shugabannin tsaro su yi murabus

Majalisar Dattawa ta bukaci Buratai da sauran shugabannin tsaro su yi murabus

- Majalisar Dattawa ta Najeriya ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro na kasar su yi murabus

- Hakan ne zuwa ne bayan wani rahoto da ke nuna sojoji fiye da 200 da ke yaki da taadanci sunyi murabus

- Majalisar ta ce shugabanin tsaron sunyi iya kokarinsu amma hakan bai wadatar ba saboda haka a nada sabbi

Majalisar Dattawa a ranar Talata ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro na ƙasar su sauka daga mukamansu saboda cigaba da tabarbarewar tsaro a ƙasar.

Majalisar ta cimma wannan matsayin ne bayan Sanata Ali Ndume, (APC, Borno) ya gabatar da kudirin nuna damuwarsa kan rahoton murabus ɗin da sojoji fiye da 200 suka yi.

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta bukaci Buratai da sauran shugabannin tsaro su yi murabus
Shugabanannin hukumomin tsaron Najeriya. Horo daga Daily Trust.
Asali: Twitter

Yan majalisar da suka tofa albarkacinsu a kan kudirin da Ndume ya gabatar sun koka kan yadda lamuran tsaro ke cigaba da tabarbarewa da kuma rashin iya gudanar da ayyukan cigaba a yankunan.

DUBA WANNAN: Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000

Sun ce jamian sojoji da dama suna tsoron rasa rayyukansu yayin yaki da taadancin hakan yasa suke barin aikin da kansu.

Mataimakin kwamitin kwastam, Sanata Ayo Fadahunsi ya bayar da shawarar shugabanin tsaron su yi murabus inda Sanata Betty Apiafi ta goyi bayansa.

Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan shima ya amince da bukatar kuma sanatoci da dama da sika hallarci zaman suma sun amince.

Majalisar ta kuma bukaci kwamitin ta na tsaro ta binciko dalilin da yasa jami'an sojojin suke yin murabus da kansu.

A jawabinsa, Lawan ya ce duk da cewa Rundunar Sojojin tana iya ƙoƙarin ta don samar da tsaro, ƙoƙarin nata bai wadatar ba saboda haka ya yi kira ga Shugaba Buhari ya nada sabbi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel