NDDC: An bawa Akpabio wa'adin awa 48 ya fada sunayen ƴan majalisar da suka karbi kwagilla

NDDC: An bawa Akpabio wa'adin awa 48 ya fada sunayen ƴan majalisar da suka karbi kwagilla

- Majalisar Wakilai ta tarayya ta kalubalanci ministan Niger Delta, Godswill Akpabio ya bayyana sunayen ƴan majalisar da ya ce sun karbi kwangila daga NDDC

- Akpabio ya yi ikirarin cewa mafi yawancin kwangilar da aka bayar a hukumar ta NDDC yan majalisa ne aka bawa

- Ministan na Niger Delta ya yi wannan zargin ne a lokacin da ya ke bayar da ba'asi gaban kwamitin bincike kan rashawa ta ake zargin an tafka a NDDC

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya bawa Ministan Harkokin Niger Delta, NDDC, Godswill Akpabio, waadin awa 48 ya wallafa sunayen yan majalisa zubi ta 9 da suka karbi kwangila daga NDDC.

Kakakin ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke martani a kan batun da shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya gabatar masa.

Mr Elumelu ya bukaci Majalisar ta gayyaci Mr Akpabio ya bayyana sunayen wadanda suka karbi kwangila daga NDDC.

NDDC: An bawa Akpabio wa'adin awa 48 ya fada sunayen yan majalisar da suka karbi kwagilla
NDDC: An bawa Akpabio wa'adin awa 48 ya fada sunayen yan majalisar da suka karbi kwagilla
Asali: UGC

Mr Akpabio a ranar Litinin yayin zaman sauraron baasi game da binciken zargin rashawa a NDDC ya yi ikirarin cewa NDDC na bawa yan majalisa kwangila.

DUBA WANNAN: Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000

Wannan batun ya tayar da hankula a wurin taron har sai da shugaban taron, Thomas Ereyitomi ya lalashe wasu yan majalisa da suka fara cacan baki da ministan.

Da ya ke martani a kan batun da Mr Elumelu ya gabatar masa, Kakakin ya ce bai ji dadin yada yan jarida suke taya shi yayata "abinda muka san ba gaskiya bane."

"Ban taba karbar kwangila ba ko sau daya daga NDDC kuma na san wasu yan majalisar da dama kamar ni," in ji Gbajabiamila.

"Saboda haka ina kira ga ministan ya wallafa sunayen yan majalisun, kwangiloli, kwanan wata da kamfanonin da ya ce an bawa kashi 60 na kwangilar ta hukumar NDDC."

Ya ce idan ko ministan bai wallafa sunayen ba majalisar ba ta da wani zabi da ya wuce su dauki matakin da doka ta tanada a kan shi.

"Haka ta rataya a kan ministan, ya sanar da kwamitin, mutanen Niger Delta da yan Najeriya wadanda aka bawa kwangilolin," a cewar Kakakin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel