Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya

Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya

- Mr Boss Mustapha Ya ce Nigeria zata fuskanci wata babbar annoba ma damar aka gaza bunkasa fannin kiwon lafiyar kasar

- Ya ce cutar Covid-19 ta fito da gazawar fannin kiwon lafiya, da gazawar gwamnati, da gazawa ta fuskar tsaro

- Babban bankin Nigeria ya ce a halin yanzu, akwai ayyuka 20 da aka kashewa akalla N26.278bn karkashin shirin tallafi ga fannin lafiya na N100bn

Gwamnatin tarayya ta ce Nigeria zata fuskanci wata babbar annoba ma damar ta kasa amfani da yanayin da annobar COVID-19 wajen bunkasa fannin kiwon lafiya.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Mr Boss Mustapha ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da hukumar kwararru (BoE) na shirin bincike da bunkasa kiwon lafiya (HSRDIS) a Abuja.

A cewar sa: "Idan har muka tsallake wannan yanayin, to lallai zamu fuskanci wata annobar kuma ba zamu iya tsinana komai ba.

"Idan da ace mun bunkasa fannin kiwon lafiya a lokacin annobar Ebola, da bamu sha wahalar da muka sha a yanzu ba, tunda cibiyoyin gwajin COVID-19 biyu kadai garemu."

Ya kara da cewa: "Idan da zaka zagaya kasar nan, zaka samu sama da cibiyoyin kiwon lafiya 10,000, amma kalilan ne ke da kayan aiki, wasu ma ba a amfani da su."

Ya roki mambobin kwamitin kwararrun da su yi bincike kan gine ginen gwamnati na kiwon lafiya banda bangaren aikin da aka dauke su.

KARANTA WANNAN: COVID-19: An soke taron bayar da kambun kwallo na Ballon d’Or 2020

Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya
Akwai sabuwar annobar da ke jiran Nigeria - Gwamnatin tarayya Source: Twitter
Asali: Twitter

Cutar COVID-19, a cewar sakataren gwamnatin tarayyar, "ta fito da gazawar fannin kiwon lafiya a kasar, da gazawar gwamnati, da gazawa ta fuskar tsaro, da matakan kariya a tsakanin al'umma."

Ya yi gargadin cewa: "Zai zama abun kunya garemu idan har bamu yi amfani da wannan lokacin wajen kawo karshen matsalolin dake addabar kiwon lafiya da gine ginenmu ba."

Gwamnan babban bankin Nigeria, Godwin Emefiele, ya ce: "A halin yanzu, akwai ayyuka 20 da aka kashewa akalla N26.278bn karkashin shirin tallafi ga fannin lafiya na N100bn."

Ya bayyana cewa "wasu daga cikin cibiyoyin da suka samu tallafin sun hada da asibitoci, cibiyoyin bincike da kuma kamfanonin sarrafa magunguna."

Sai dai, darakta sashen bunkasa kudi na CBN, Mr. Philip Yila Yusuf ya bayyana cewa CBN ta samu bukatu 27 daga masu bincike dake bukatar tallafin N67bn.

Tallafin kudin zai taimaka masu wajen samar da rigafi, bunkasa karfin magunguna da samar da kayayyaki daban daban da zasu taimakawa Nigeria wajen magance matsalolin da ke addabar fannin kiwon lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel