Da duminsa: An saki Ibrahim Magu

Da duminsa: An saki Ibrahim Magu

An saki dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, kamar yadda jaridar Premiun Times ta wallafa da yammacin yau, Laraba, 15 ga wata Yuli, 2020.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa an saki Magu ne da yammacin ranar Laraba bayan ya shafe kwanaki 10 a tsare.

Sai dai, ya zuwa yanzu Premium Times ba ta wallafa karin bayani dagane da sakin Magu da aka yi ba.

Amma, jaridar TheCable ta wallafa cewa ''duk da bayanan sharudan bayar da belin Magu sun yi wuyar samu, majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa ya koma gidansa."

Wannan shine mako na biyu da fara binciken Magu bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa.

Tun bayan fara gurfanarsa a gaban kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa, Magu bai koma gida ba, ya na tsare a hedikwatar rundunar 'yan sanda ta kasa, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.

Magu ya fara gurfana a gaban kwamiti bincike a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, kuma tun daga ranar wasu jami'an 'yan sanda su ka yi awon gaba da shi zuwa hedikwatarsu.

Jami'an 'yan sanda ne su ke kai Magu fadar shugaban kasa duk lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin bincike domin cigaba da amsa tambayoyi a kan tuhume - tuhumen da ake yi masa.

Da duminsa: An saki Ibrahim Magu
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, ya sanar da Ibrahim Magu cewa ba shine keda alhakin tsarewar da aka yi masa ba.

Tosin Ojoamo, lauyan Magu, ya rubuta takardar neman belin Magu zuwa ofishin babban sifeton rundunar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Handame N1.5bn: Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA shekaru 7 a gidan kaso

Sai dai, a cikin wasikar martani mai lamba CB: 7000/IGP/.SEC/ABJ/VOL.489/171 da IGP ya aikawa lauyan Magu, ya sanar da shi cewa ya karkata akalar bukatarsa zuwa gaban kwamitin da ke binciken zarge - zargen da ake yi wa Magu.

IGP ya aikawa Ojoamo wasikar ne a ranar Talata, 14 ga watan Yuli, 2020, kwanaki hudu bayan lauyan ya aika wasikar neman belin Magu.

Wani bangare na wasikar ya bayyana cewa; "IGP yana son jan hankalinka a kan cewa rundunar 'yan sanda ba ta binciken C.P. Ibrahim Magu (mutumin da ka ke wakilta), kwamitin shugaban kasa da ke binciken harkokin hukumar EFCC ne ya ke bicikensa.

"A saboda haka, IGP yana shawartarka ka karkatar da bukatarka zuwa shugaban kwamitin bincike domin samun amsar da ta dace."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel