Za mu kashe N3bn domin yakar zazzabin cizon sauro a Kano - Ganduje

Za mu kashe N3bn domin yakar zazzabin cizon sauro a Kano - Ganduje

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya kaddamar da shirin bayar da tallafi ga mata masu juna biyu da kuma kananan yara.

Haka kuma Ganduje ya kaddamar da shirin yi wa kananan yara da ba su wuce watanni uku zuwa shekaru biyar da haihuwa ba allurar rigakafin zazzabin cizon sauro.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa tare da hadin gwiwar kungiyar Malaria Consortium, ta ware naira biliyan 3 da za ta batar domin tabbatar da nasarar wannan shiri da ta kaddamar.

Furucin gwamnan ya zo ne a ranar Lahadi yayin da ya ke kaddamar da shirin a karamar hukumar Bichi da ke shiyyar Kano ta Tsakiya.

Gwamnan Kano tare Sarkin Bichi yayin kaddamar da shirin a garin Bichi
Gwamnan Kano tare Sarkin Bichi yayin kaddamar da shirin a garin Bichi
Asali: Twitter

Gwamnan Kano tare Sarkin Bichi yayin kaddamar da shirin a garin Bichi
Gwamnan Kano tare Sarkin Bichi yayin kaddamar da shirin a garin Bichi
Asali: Twitter

Gwamnan Kano yayin kaddamar da shirin a garin Bichi

Ganduje yayin jaddada daurin damarar da ya yi, ya ce yawaitar matsalar zazzabin cizon sauro musamman a wannan lokaci na damuna, ita ta sanya gwamnatinsa ta mike tsaye domin tunkarar lamarin.

Ya ce gwamnatinsa ta karkatar akalar hankali tare da bayar da fifiko a kan rigakafin cutar zazzabin cizon sauro da sauran cututtukan da ke kassara yara.

Kamar yadda Gidan Talibijin na kasa NTA ya ruwaito, Ganduje ya sake jaddada muhimmancin da gwamnatinsa ta bai wa lafiyar mata masu juna biyu da kuma kananan yara, lamarin da yake jan hankalin iyaye a kan basu hadin kai.

Ganduje ya lura da yadda duniya ta rudu tare da mayar da hankali a kan dakile yaduwar annobar korona, ya ce ita kuwa gwamnatinsa ta daura damarar tunkarar wasu cututtukan na daban.

KARANTA KUMA: Ana samun ƙaruwar auren wuri saboda rashin inganta tsarin ilimi - Sarki Sanusi

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta bullo da ingantattun shirye-shiryen na bunkasa harkar kiwon lafiya da ke mai da hankali kan sauran cututtuka.

A nasa jawaban, kwamishinan lafiya na jihar Dr. Aminu Tsanyawa, ya ce wannan shiri da gwamnatin ta kaddamar zai yadu a dukkanin kananan hukumomi 44 da ke fadin Kano.

Dakta Tsanyawa ya yi bayanin cewa, za a rika gudanar da wannan shiri cikin kwanaki hudu na kowane wata tun daga watan Yuli har zuwa Oktoban shekarar da muke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel