Dakarun soji sun ceto mutum 3 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu

Dakarun soji sun ceto mutum 3 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutum 3 da aka yi garkuwa dasu a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce dakarun sojin ne karkashin rundunar Operation Thunder Strike na kasan Operation Accord, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kakakin rundunar ya yi bayanin cewa bayanan sirrin da sojojin suka samu ne na cewa 'yan bindiga sun sace wasu mutane a gonarsu da ke kauyen Gwazunu, yasa suka bi sahu.

Ya kara da cewa jami'an tsaro da aka tura da gaggawa ne suka yi musayar wuta tsakaninsu da 'yan bindigar.

"Yan bindigar sun tarwatse tare da raunika sakamakon harbin da suka sha. A nan ne suka hada wadanda suka yi garkuwa da su.

"Dukkan wadanda aka sacen an samesu babu wani rauni kuma sun hadu da 'yan uwansu," Enenche yace.

Kamar yadda yace, rundunar na taya zakakuran sojin murna a kan jajircewarsu tare da kira garesu da su ci gaba da mayar da hankali don ganin bayan 'yan ta'adda a yankin.

Dakarun soji sun ceto mutum 3 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu
Dakarun soji sun ceto mutum 3 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651

Kamar yadda ya sanar, a ci gaban tabbatar da kawo zaman lafiya da dakarun sojin Najeriya ke yi, rundunar Operation Hadarin Daji karkashin Operation Accord a ranar 7 ga watan Yulin 2020, ta hadu da 'yan bindiga a karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto.

A yayin amfani da salon iya yaki, dakarun sunyi musayar wuta da 'yan bindigar, inda suka kashe biyu daga ciki. Wasu daga ciki sun tsere da raunika sakamakon harbin bindiga.

Hakazalika, a ranar 8 ga watan Yuli 2020, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri a kan kaiwa da kawowar 'yan bindigogi masu tarin yawa. Sun tsaresu a yayin da suke tafiya da shanun sata zuwa kauyen Jangemi da ke kusa da garin Kwaren Ganuwa.

Tuni dakarun suka tsare 'yan bindigar a kauyen Bawaganga. Bayan ganin dakarun da suka yi, sun tsere inda suka shiga dajin Muhaye tare da barin shanu 250 da raguna 150.

A halin yanzu ana tsare da dabbobin. A wani ci gaba da ya faru a ranar 8 ga watan Yulin 2020, dakarun sun kai samame wurin Kwaren Ganuwa da ke kusa da Tsafe inda suka samo dabbobi masu tarin yawa.

'Yan bindigar sun tsere bayan ganin dakarun. Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar sojin, John Eneche ya fitar a wata takarda, ya ce a ranar dakarun sun samo shanu 117 da tumaki 34.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel