Magu ya nemi beli a wurin IGP

Magu ya nemi beli a wurin IGP

Dakatattacen mukadashin shugaban yaki da rashawa ta EFCC, Mr Ibrahim Magu da ake bincika a kan zargin rashawa ya nemi Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar da shi beli.

Kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa karkashin jagorancin tsohon alkalin kotun koli Ayo Salami ne ke bincikar Magu.

Magu, wanda aka tsare tun ranar Litinin ya rubuta wasika ta hannun lauyansa, Mr Oluwatsosin Ojaomo a ranar Juma'a zuwa ga IG na neman beli kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Magu ya nemi beli a wurin IGP
Magu ya nemi beli a wurin IGP. Hoto The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Tun ranar da aka kama shi, Magu yana tsare ne a wani wurin ajiya na rundunar 'yan sanda a Abuja inda daga nan ya ke zuwa gurfana gaban kwamitin binciken.

Wasikar da lauyansa ya rubuta zuwa ga ofishin IGP mai dauke da kwanan wata na 10 ga watan Yuli kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito ta nemi a bayar da shi beli, "bisa sanayar da aka masa a kasa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel