Magu: Kwamitin bincike ya umarci daraktocin EFCC su kawo rahoton ayyukansu na shekaru 5
Wasu daraktocin hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da wasu manyan jami'an hukumar, a ranar Alhamis sun bayyana gaban kwamitin bincike.
Kwamitin binciken ya samu jagorancin Mai shari'a Ayo Salami a kan zargin rashawa da ake wa dakataccen shugaban hukumar, Ibrahim Magu.
Daga cikin wadanda suka bayyana gaban kwamitin akwai sakataren EFCC, Olanipekun Olukoyede.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, an bincikesu na fiye da sa'o'i 12. An gayyacesu ne don su bada abinda suka sani game da wasu zargi da ake wa Magu.
An bukaci dukkan shugabannin sashe na hukumar da su je su hada rahoton dalla-dalla na ayyukansu tun daga 2015, lokacin da aka nada Magu har zuwa ranar Alhamis.
Wata majiya ta ce Magu ya sake bayyana gaban kwamitin a ranar Alhamis, amma an bukaci ya bar wurin a lokacin da aka kira daraktan ayyuka, Mohammed Umar, don ya bada shaida.
KU KARANTA: Hushpuppi: Dubai ta tsame 'yan Najeriya daga neman aiki tare da samun Visar shakatawa
Majiyar ta bukaci kowanne shugaban sashe da yasa hannu a kan kowanne shafin rahoton da za su gabatar.
Wadanda suke sashen kwace kadarori kuwa an bukaci su hada da rasit tare da lambar kowacce kadara da suka karba.
"Kamar yadda alamu suka bayyana, an gano cewa kwamitin za su bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan yadda za a shugabanci hukumar," wata majiya tace.
An gano cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar Ondo, wanda ya taba aiki a karkashin EFCC ya bada shaida a gaban kwamitin.
Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, na sake fuskantar kalubale da zargi. Ana zarginsa da mallakar kadarori a Dubai.
Dakataccen shugaban EFCC, wanda ke hannun 'yan sanda tun daga ranar Litinin, an ci gaba da tuhumarsa a ranar Laraba.
Jaridar The Punch ta gano cewa, wani sabon zargi ya bullo bayan zaman ranar Laraba, lamarin da yasa aka sake tsaresa.
Jami'an tsaron farin kaya ne suka tsare Magu a gaban tsohuwar hedkwatar EFCC da ke titin Fomella, Wuse 2 a Abuja, a ranar Litinin kuma suka tasa keyarsa zuwa fadar shugaban kasa.
Yana ofishin 'yan sanda da ke Garki tun daga ranar Litinin inda daga nan aka mika shi fadar shugaban kasa don ci gaba da bincikarsa.
Kamar dai yadda al'amarin ranar Litinin da Talata ya faru, an ci gaba da tuhumar Magu amma an hana manema labarai shiga wurin ko a ranar Laraba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng